Aminiya:
2025-04-14@18:14:56 GMT

Aisha Binani ce ta lashe zaɓen Adamawa, ina da ƙwararan hujjoji – Ari

Published: 9th, February 2025 GMT

Tsohon Kwamishinan Zaɓe na Jihar Adamawa, Hudu Ari, ya ce bai damu da korar da aka yi masa ba, amma yana nan a kan bakansa cewa Aisha Binani ta jam’iyyar APC ce, ta lashe zaɓen gwamna na 2023.

An dakatar da Hudu Ari bayan da ya ayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen tun kafin a kammala tattara sakamakon ƙuri’u.

Gobara ta ƙone motoci da shaguna a wajen sayar da gas a Neja Taron Qur’ani: Tsakanin magoya baya da masu kushe

Sai dai ya ce yana da hujjojin da ke nuna cewa Binani ta doke Gwamna Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP.

Da yake magana da manema labarai a Bauchi, Ari ya rantse da Alƙur’ani mai girma cewa manyan jami’an zaɓe sun yi watsi da hujjojinsa kan maguɗin zaɓe.

Ya zargi shugaban sashen Kimiyya da Fasaha na INEC a Adamawa da yin aringizon ƙuri’u, sannan jami’an tsaro sun kama wasu jami’an gwamnati suna canza sakamakon zaɓe.

Ari ya kuma zargi shugaban INEC da kotun zaɓe da yin watsi da bayanansa.

Ya ce ba a ba shi damar kare kansa ba, ko kuma tuntuɓar iyalansa domin yanke shawarar ɗaukar matakin shari’a.

Ya ce bai damu da korarsa daga aiki da aka yi ba, illa ɓata masa suna da aka yi a kafafen yaɗa labarai.

Ya ƙara da cewa rayuwarsa ta shiga hatsari yayin da ake gudanar da zaɓe, inda ya bayyana yadda shi da wasu jami’an zaɓe aka yi musu barazana don su ayyana gwamna mai ci a matsayin wanda ya lashe zaɓen jihar.

A cewarsa, an janye masa tsaro bayan ya ƙi amincewa da buƙatar.

Duk da cire shi daga muƙaminsa, Ari ya dage kan cewar ya bi dokokin zaɓe kuma ya yi abin da ya dace.

Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su kasance masu gaskiya da adalci a lokacin zaɓe, tare da gargaɗin cewa rashin yin hakan zai iya jefa dimokuraɗiyya cikin wani hali.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Hudu Ari Maguɗin Zaɓe Zaɓen

এছাড়াও পড়ুন:

Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya

A ranar Lahadi Liverpool ta sake matsa ƙaimi a gasar Firimiya bayan ta doke abokiyar karawarta West Ham United ci 2-1 a filin wasa na Anfield dake birnin Liverpool, yayin da Mohamed Salah ya kafa tarihin cin ƙwallaye a kakar wasa ta bana, sakamakon ya sa Liverpool ta samu tazarar maki 13 tsakaninta da Arsenal dake matsayi na biyu a kan teburin gasar.

Yayinda yake saura wasanni shida a kammala gasar, Liverpool na buƙatar maki 3 kacal domin lashe gasar a karo na biyu tun bayan da aka sauya wa gasar suna da fasali, West Ham na matsayi na 17 da maki 35 akan teburin gasar.

Ba Zan Ci Gaba Da Zama A Liverpool Ba -Salah Salah Ya Ƙulla Sabuwar Yarjejeniyar Shekaru 2 Da Liverpool

ESPN ta ruwaito cewa kafin fara wasan, an yi shiru na minti daya a Anfield don nuna girmamawa ga mutane 97 da iftila’i ya rutsa da su a filin wasa na Hillsborough a shekarar 1989, sai dai magoya bayan Liverpool sun ɓarke da ihu jim kaɗan bayan shirun, inda suke nuna jin daɗinsa dangane da sabon kwantiragin shekaru biyu da Salah ya sanya hannu a tsakiyar mako.

A wannan wasan ne Salah ya kafa tarihin wanda ya fi zama komai da ruwanka a wajen zura ƙwallaye a raga a wasannin gasar inda ya zura ƙwallaye 27 ya kuma taimaka aka jefa 18, ana alaƙanta Salah da komawa ƙasashen Larabawa domin cigaba da taka leda, amma kuma sabon kwantiragin da Salah ya sakawa hannu ya sa zai cigaba da zama a Anfield tsawon shekaru biyu.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Aljeriya ta yi barazanar korar jami’an diflomasiyyar Faransa 12
  • ‘Yansanda Sun Kama Wani Kato Bisa Zargin Cin Zarafin Wata Mata A Adamawa
  • A Kasar Gabon Brice Oligui Nguema Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa
  • Brice Ologui Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Gaban Da Kashi 90.35% A Jiya Lahadi
  • Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya
  • Badaƙalar Miyagun Ƙwayoyi: Kotun Amurka ta ba da umarnin fitar da bayanai kan binciken Tinubu
  • Mutum ɗaya ya mutu a faɗan ƙungiyar asiri a Maiduguri
  • Kashe-kashen Filato: Jami’an tsaro na sassauta wa masu laifi —Tsohon gwamnan soji
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassa Al-Mujtaba (a) 107
  • Atiku ya jagoranci manyan ’yan siyasa sun ziyarci Buhari