Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na sharhin bayan labarai, wanda zai yi magana a kan “Yadda JMI Ta Bunkasa Sana’argine-gine da da kamfanoni tare da amfani da fasahar cikin gida’ wanda ni tahir amin zan karanta.

Tun bayan nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran a shekara 1979, daya daga cikin bangarorin da aka sami gagarumin ci gaba a cikinsa shi ne, bunkasa sana’ar gine –gine da kuma samar da masana’antu, wanda ya kai ga kasar ta kai ga wadata a wannan bangaren, wani abu daga kasashen waje, sai abunda ba za’a rasaba.

Har’ila yau wannan ya wadanar da mutane da dama a kasar.

Kafin haka idan mun dubi kasar Iran kafin juyin juya halin musulunci a kasar, zamu ga cewa kusan duk wani al-amari ya shafi gine-gine na hanya gadoji asbito ci, da gidaje . Haka ma masana’antu sun dogara kacokap kan kasashen waje musamman Amurka.

A cikin rabin karni na 20TH bayan an sami arzikin man fetur a kasar Iran, ci bayan da kasar ta yi ya sa da dogara da kasashen waje musamman Amurka do samar da hanyoyi da layukan dogo da gadaje da madatsun ruwa da gine-ginen zamani a manya manyan biranen kasar. Muna iya cewa dukkan manya-manyan ayyuka kamfanonin kasashen waje ne suke gana su, ba’abinda ira niyawa zasu iya yi sai ayyukan karfi da wasu wadanda basu da muhimmanci sosai.

A tsakanin shekara 1960-70, kamfanonin Amurka ne suka mamaye mafi yawan ayyukan ginegine a kasar Iran. Sannan a lokacin yakin cacan baki Amurka ce da mamaye dukkan harkokin tsaron kasar Iran. Da kuma kamfanonin haka da sarrafa man fetur.

A lokacinda farashin danyen man fetur ya tashi Amurka ta yi kokarin ginin dukkan kudaden sun koma kasar Amurka. Barin talakawan Iran hannu banza, duk tare da kudaden da suka shiga hannun gwamnatin kasar.

Abubuwan da kwararru na cikin gida suka yi ya kara fallasa barnan da kamfanonin kasashen waje suka yi a kasar. Sannan takunkuman Amurka sun sanya wasu ayyukan ma gaba daya an daina su sabo kayakin aikin daga waje ake zuwa da su.

Don haka a cikin wannan halin kwararru na cikin gida suna kammala rukunin gidaje na Ecbatona a birnin Tehran wanda wani kamfanin amurka ya fara ginashi bai kare ba aka yi juyin juya hali ya bar aikin rabi da rabi.

Sannan bayan yaki na shekaru 8 gwamnatin Rafsanaja ta samar da shirin sake gina kasar wanda ya kawo sauyi mai yawa a bangaren gine-gine a ko wani bangaren a kasar. Wadanda suka hada da manya-manyan tituna rukunan gidaje, layukan dogo sabbin tasoshin jiragen sama da jiragen ruwa, madatsun ruwa da kayakin lantarku da sauransu.

Daga cikin matakan da sabuwar gwamnatin JMI ta dauka don warware matsalilin gidaje, a iran. Akwai basusuka masu sauki, kula da farashin kayaki, da rage farashin wasu kayaki musamman abinda don talaka ya samu, sannan rarraba filaye don gina gidaje da farashin mai rahusa.

Kodaitar da manya-manyan kamfanoni su karfafa kananan kamfanoni, ko daddaikun mutane da sauransu.

An yada shi’arin cewa , al-amuran kasar Iran ba zai sake komawa cikin hannun yan waje ba,.

Tare da wannan sai kamfanonin cikin gida suka kammala manya manyan ayyuka wadanda kamfanonin kasashen waje suka fara yi, basu karasa ba, sai suka fara sabbin gine-gine, wadanda suka sauya fuskar biranen Iran musamman a birnin Tehran.

Shekaru 46 da suka gabata, mafi yawan kasar Iran kauyuka ne, mafi yawan mutane suna rayuwa a kauyuka, amma a halin mafi yawan kasar Iran rayuwar birane suke, wanda ya tashi daga kashi 48 zuwa 77 %.

Daga lokaci zuwa yanzun an samar da birane kimani 1,300, daga 373 kacal kafin nasarar Juyin juya halin musulunci.

Kuma ana amfani da kayakin gini masu karfi ganin kasar tana fama da yawan girgizan kasa. Don haka a halin yanzu girgizan kasa mai ma’auninriche 5-7 ba zasu yi barna mai yawa ba, saboda ingancin gine gine.

Banda wannan Iran ta kai matsayinda a wasu bangarori ta shiga cikin kasashe 10 masu samar da misali ceminta da karafa a duniya. Sannan tana sayar da su ga kasashen waje. A bangare kayakin kawa sai kasar Chaina da indiya ce suke gabanta. Masu sauraro karshen sharhin bayan labaran Kenan.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: a manya manyan kasashen waje

এছাড়াও পড়ুন:

Nijar, Burkina Faso da Mali sun fice daga kungiyar kasashe renon Faransa

Kasashen Nijar da Burkina Faso da kuma Mali kowannensu sun sanar da ficewa daga kungiyar kasashe renon faransa ta (OIF).

Nijar ta sanar da ficewa daga kungiyar a ranar Litini, yayin da Mali ta bi sahu a ranar Talata, aa daidai lokacin da ake raya makon kungiyar.

Babban sakataren ma’aikatar harkokin wajen kasar Laouali Labo, a wata wasika da ya aikewa jakadun kasar ya ce: “Gwamnatin Nijar ta yanke shawarar ficewa daga kungiyar ta OIF.”

Nijar dai na daga cikin kasashen da suka asassa kungiyar ta OIF, wacce aka kafa a Yamai babban birinin kasar a ranar 20 ga watan Maris na shekarar 1970, kuma tsohon shugaban kasar Dojori Hamani na waccen lokacin na daga cikin jagororin da suka kafa kungiyar.

To saidai dangankata ta yi tsami tsakanin faransa da sojojin dake mulki a kasashen guda uku a baya bayan nan.

Kungiyar ta OIF, “maimakon tallafawa wadannan kasashe wajen cimma manufofin raya al’ummarsu, (…) ta kauce wa hanya inda ta sanya siyasa a cikin lamuranta,” in ji ministocin harkokin wajen kawancen kasashen guda uku na Sahel a wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a yammacin jiya Talata.

Kungiyar ta OIF, da ta hada kasashe da gwamnatoci 93, manufarta ita ce inganta harshen Faransanci da raya al’adu, don ƙarfafa zaman lafiya, da dimokuradiyya da ‘yancin dan adam, don tallafawa ilimi, horo da bincike, da kuma inganta hadin gwiwar tattalin arziki don samun ci gaba mai dorewa.

Sai nan da watanni shida masu zuwa ne ficewar kasashen za ta tabbata.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran da UAE sun kirayi Isra’ila da Amurka da su kawo karshen hare-harensu a Gaza da Yemen
  •  HKI: Ana Samun Koma Bayan Sojojin Sa-Kai Da Suke
  • Nasiru Ahali Shahararren masanin masana’antu a Kano ya rasu
  • Gwamna Yusuf Ya Yi Sabbin Nade-Nade A Kano
  • Iran: Jagora ya yi kira da a karfafa dogaro da kai a cikin gida domin dakile tasirin takunkumai
  • Iran Ta Kira Jakadun Kasashen Jamus da Butaniya Zuwa Ma’aikatar Harkokin Waje Don Jan Kunnensu
  • Alakar Tattalin Arziki Da Cinikayya Bisa Daidaito Tsakanin Sin Da Amurka Za Ta Amfanar Da Kamfanonin Duniya
  • Sabon Kawancen Jihohin Arewacin Najeriya Da Kamfanonin Sin Zai Fa’idantar
  • Iran : hare-haren Isra’ila a Gaza ci gaba da kisan kare dangi ne
  • Nijar, Burkina Faso da Mali sun fice daga kungiyar kasashe renon Faransa