Alkaluman Farashin Kayayyaki A Sin Sun Karu Zuwa Kaso 0.5 A Janairu
Published: 9th, February 2025 GMT
Alkaluman farashin kayayyakin masarufi na kasar Sin (CPI), wanda ke auna matakin hauhawar farashin kayayyakin, sun daga da kaso 0.5 bisa dari a watan Janairu.
Adadin ya karu ne kan kaso 0.1 bisa dari da ya kasance a baya, galibi saboda hutun bikin bazara na sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin, a cewar hukumar kididdigar kasar.
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Birnin Istambul Ta Dakatar Da Akram Imamoglu Daga Matsayinsa Na Magajin Garin Birnin
Hukumar birnin istambul ta bada sanarwan dakatar da Akram Imamoglu daga matsayinsa na magajin garin birnin Istambul na wucin gadi, har zuwa lokacinda za’a tabbatar da kubutarsa daga abubuwan da aka zarginsa da su.
Tashar talabijin ta Almayaddeen ta kasar Labanon ta nakalto mahukunta a birnin Istambul na bada labarin cewa za’a zabi wanda zai maye gurbinsa na wucin gadi a ranar Laraba mai zuwa.
Labarin ya kara da cewa ana zirgin Imamoglu da karban rashawa da cin hanci da kuma kafa kungiyar yan ta’adda.
Kama Imamoglu magajin garin na birnin Istambul dai a makon da ya gabata, ya sa dubban daruruwan masu goyon bayansa a birnin Istambul da wasu birane a kasar suka fito kan tituna tare da bukatar a sake shi.
Ana ganin Imamoglu zai iya zaman dan takarar shugaban kasa wanda zai iya kada shugaba Ordugan a zaben shugaban kasa mai zuwa.