Kwamandan Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Ya Ce: Hamas Ta Yi Rawar Gani Wajen Kare Kanta
Published: 10th, February 2025 GMT
Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Kungiyar Hamas duk da iyakantaccen kayan yakinta ta kalubalanci gwamnatin ‘yan sahayoniyya
Kwamandan dakarun kasa na Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Morteza Miryan ya jaddada cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta kalubalanci gwamnatin mamayar ‘yan sahayoniyya da suke samun goyon bayan Amurka da kasashen Yamma duk da iyakantaccen kayan yakin da ta mallaka na kare kai.
Birgediya Janar Miryan ya ce a cikin jawabinsa a wajen bikin tunawa da shahidan harin “Wal-Fajir 8” da aka gudanar a lokacin tunawa da shahidan lardin Alborz da ke yammacin birnin Tehran: A lokacin yakin da aka yi na shekara ta 1980 zuwa shekara ta 1988), yana cewa; A lokacin yakin sun ga yadda gwamnatin Saddam na Iraki ta mallaki dukkan nau’o’in makamai, amma kuma al’ummar Iran suka tsaya tsayin daka wajen yaki da ta’addanci.
Yayin da yake nuni da laifuffukan da yahudawan sahayoniyya suke yi a yankunan Falastinu da suka mamaye, Birgediya Janar Miryan ya ce: Duniya ta taimaka wa ‘yan sahayoniyya ‘yan mamaya, kuma dukkanin tsarin makaman sararin samaniyya suna hannunsu, amma kungiyar Hamas ta tsaya tsayin daka da karfinta.
Janar Miryan ya kara da cewa: A yayin harin daukan fansa na “Alkawarin Gaskiya na 1 da na 2, Iran ta tabbatar da cewa: Kashi 85 cikin 100 na makamai masu linzaminta sun kai ga inda aka saita su.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sudan: Sojoji na ci gaba karbe mahimman gine-gine a birnin Khartoum
A Sudan bayan sake karbe fadar shugaban kasa da ke birnin Khartoum, sojojin kasar sun ci gaba da kai farmaki a babban birnin kasar a ranar Asabar, inda suka sake karbe iko da wasu gine-gine, ciki har da babban bankin kasa da hedkwatar hukumar leken asiri da kuma gidan adana kayan tarihi na kasar.
Ana kallon wannan a matsayin nasarorin ga Janar al-Burhan a babban birnin kasar, wanda rikicin cikin gida ya rutsa da shi na tsawon shekaru biyu.
A wannan Asabar, kakakin rundunar sojojin kasar, Janar Nabil Abdullah, ya sanar a cikin wata sanarwa cewa sojojin na ci gaba da samun nasara a birnin Khartoum, Ya kuma ce sojojin sun “kore daruruwan ‘yan bindiga.
A sa’i daya kuma, ana ci gaba da gwabza fada a yankin Darfur, wanda kusan yana karkashin ikon dakarun RSF.
A cewar masu fafutukar kare hakkin jama’a, akalla fararen hula 45 ne aka kashe a ranar Alhamis a wani harin da dakarun sa kai suka kai a garin Al-Malha da ke arewacin Darfur.
Sojojin sun yi ikirarin cewa sun yi wa garin kawanya tare da kashe makiya sama da 380.