Aminiya:
2025-04-16@09:21:54 GMT

NAJERIYA A YAU: Shin Har Yanzu Akwai Masu Rufin Asiri A Najeriya?

Published: 10th, February 2025 GMT

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Akan karkasa mutane gida-gida a bisa mizanin tattalin arziki, musamman a tsarin jari-hujja, inda ke da mawadata da kuma matalauta.

A tsakanin al’umma kuma akwai ajin mutane masu matsakaicin samu waɗanda ake kira “Middle Class”.

Akan sanya mutane a wannan aji ne galibi bisa la’akari da aiki ko sana’ar da suke yi, da kuɗin da suke samu, da matakin ilimin da suka kai, da ma matsayinsu a tsakanin al’umma.

Sai dai a baya-bayan nan irin wadannan muntane sun bi sahun matalauta wajen korafi game da yadda suke dandana kudarsu saboda tsadar rayuwa.

NAJERIYA A YAU: Dalilin Faɗuwar Farashin Tumatur A Kasuwa DAGA LARABA: Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma ‘Event Centre’

Shin a iya cewa har yanzu akwai wannan aji na mutane a Najeriya ke nan?

Wannan ne batun da shirin Najeriya  a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Najeriya Tattalin Arziki

এছাড়াও পড়ুন:

 Tsoffin Ma’aikatan Hukumar Leken Asiri HKI  Mosad Sun Shiga Cikin Masu Kiran A Kawo Karshen Yaki Da Gaza

A daidai lokacin da ake ci gaba da takaddama a HKI dangane da wasikar da wasu sojojin sama su ka rubuta na sukar yakin Gaza, wasu tsoffin ma’aikatar hukumar leken asiri ta “Mosad” sun bi sawunhu.

Kafafen watsa labarum HKI sun ambaci cewa, fiye da tsoffin jami’an leken asirin kungiyar MOSAD 200 ne su ka rattaba hannu akan wata takarda suna nuna goyon bayansu da sojan sama da su ka yi kira a kawo karshen yakin Gaza.

Kwanaki kadan da su ka gabata, tashar talabijin din Channel 13; ta watsa labarin da yake cewa; Wasu ma’aikatar rundunar leken asiri ta soja sun shiga cikin masu kira da a kawo karshen yakin na Gaza da kuma dawo da fursunoni daga can.

An kuma samu irin wannan halayyar ta yin kira a kawo karshen yakin a tsakanin likitocin soja su 100 sai kuma malaman jami’a su ma daruruwa.

Kiraye-kirayen da sojojii suke yi a HKI da na kwo karshen yakin Gaza da mayar da fursunonin yaki, ya bude wata sabuwar takaddama a tsakanin ‘yan  siyasa.

Wasikar ta bude jayayya a tsakanin ‘yan sahayoniya akan cewa, Netanyahu yana ci gaba da yin yaki ne saboda maslahar kashin kansa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan Najeriya sun koka kan rashin ingancin shinkafar Gwamantin Tarayya
  • Jama’a sun koka kan rashin inganci shinkafar Gwamanti a Kogi
  • An Kashe Mutane Da Dama A Tsakiyar Najeriya
  • NAJERIYA A YAU: Dalilan Rikice-Rikice A Jihar Filato
  • Kamata Ya Yi Amurka Ta Kara Kokarin Gyara Kuskurenta 
  • Shugaba Tinubu Ya Yi Allah-wadai Da Harin Jihar Filato
  •  Tsoffin Ma’aikatan Hukumar Leken Asiri HKI  Mosad Sun Shiga Cikin Masu Kiran A Kawo Karshen Yaki Da Gaza
  • NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar Borno
  • Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Makiya Suna Hasadan Ci Gaban Kasar Iran
  • A daina cutar ’yan Najeriya ta hanyar rabon kayan tallafi