’Yan sanda sun ba al’ummar Sheka awa 24 su kawo sunayen ’yan daba
Published: 10th, February 2025 GMT
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano ya ba al’ummar yankin Sheka awa 24 su kawo wa rundunar sunayen manyan ’yan daban da ke addabar yankin.
Rundunar ta ba da wannan wa’adin ne bayan matsalar ’yan daba ta ya ƙi ci ta ƙi cinyewa a yankin da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso.
A yayin wani zama na musamman da kwamishinan rundunar ta yi da al’ummar yankin ne aka ba su wannan sanarwar.
Kwamishinan ’yan sandan, wanda ya samu wakilci DPO na yankin Dakata, ACP Yusha’u Mus’ud, ya ce muddin al’umma ba su taimaka da bayanan jagororin ’yan daban ba, ta ɓata-garin an kama su ba, babu yadda za a yi ɓata-garin su daina addabar yankin.
Ɗan fashi ya yi wa ɗaliban jami’a uku fyaɗe NAJERIYA A YAU: Shin Har Yanzu Akwai Masu Rufin Asiri A Najeriya?উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda yan daba bata gari
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Da Sifaniya Sun Daga Matsayin Hadin Gwiwa A Fannin Shirya Fina-finai
Wannan gargadi da Sin da EU suka gabatar ga manyan kamfanonin shirya fina-finai da na fasaha na Amurka, na nuna cewa, gangancin da gwamnatin Amurka ke yi na kakaba haraji barkatai, zai ci gaba da illata kashin bayan fannoninta na cinikayya.
Hadin gwiwa tsakanin Sin da Sifaniya, ya kara bayyana yadda Sin ke fatan ci gaba da bude kofarta, da aiki tare da abokan hulda irinsu Sifaniya wajen goyon bayan tsarin cudanyar sassa daban daban, da goyon bayan dunkulewar salon raya tattalin arziki da cinikayya marar shinge, da samar da karin hidimomi, da kayayyaki masu inganci ga kasashen biyu ta hanyar hadin gwiwa da juna, da mutunta juna, da amfanar da al’ummunsu. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp