’Yan daba sun ƙona gine-ginen makaranta a Binuwai
Published: 10th, February 2025 GMT
Wasu ’yan daba sun gine-ginen makaranta a yankin Okpoga da ke Karamar Hukumar Okpogwu da ke Jihar.
Ɓata-garin sun ƙona gine-ginen ne a Makarantar Sakandaren Central UBE da ke Ogwu-Okpoga da kuma Makarantar Ƙaramar Sakandare s ake Obossa.
Wani shaida ya bayyana wa wakilinmu cewa a makon da ya gabata ne ’yan daban suka yi wannan aika-aika.
Kokarinmu ma ji daga kakakin ’yan sanda ta Jihar Binuwai, Catherine Aneneh, bai yi nasara ba, saboda mun kira ta a waya ba ta shiga ba.
’Yan sanda sun ba al’ummar Sheka awa 24 su kawo sunayen ’yan daba Ɗan fashi ya yi wa ɗaliban jami’a uku fyaɗe NAJERIYA A YAU: Shin Har Yanzu Akwai Masu Rufin Asiri A Najeriya?Amma a ƙarshen mako ɗan Majalisar Dattawa mai wakiltar Binuwai ta Kudu kuma Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Abba Moroh, ya ziyarci makarantun da abun ya shafa a ƙarshen mako.
Abba Moroh ya yi tir da lamarin tare da mamakin dalilin ƙona cibiyoyin ilimi da ake rainon manyan gobe.
Daga nan sai ya yi alƙawarin sake gina ajujuwan yana mai kira ga al’ummar yankin da su tashi domin kare ababen more rayuwar da aka samar musu.
Dan majalisar ya kuma ziyarci babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Yankin Okpoga, inda ya jinjiya musu bisa ƙoƙarinsu na kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Sai dai ya koka bisa mummunan halin da ofishin yake ciki, sannan ya yi alƙawarin yi masa kwaskwarima.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Iran Ta Bayyana Cewa Kakaba Takunkumi Kan Kasarta Ya Sabawa Hikimar Gudanar Da Zaman Tattaunawa Da Ita
Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ta bayyana cewa; Kakaba takunkumi kan kasarta ya sabawa ikirarin Amurka na yin shawarwari da ita
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan matakin da Amurka ta dauka na kakabawa wasu gungun mutane masu alaka da bangaren makamashi, man fetur da iskar gas da kuma wasu mutane da dama masu fafutuka a shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na lumana takunkumi.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Baqa’i ya bayyana manufar takunkuman da Amurka ta kakabawa al’ummar Iran da cewa; A fili take nuna kyama ga masu yanke shawaran Amurka kan al’ummar Iran da kuma nuna rashin mutunta doka da hakkin dan Adam ne.
Ya kara da cewa: Dogaro da tsarin gwamnatocin Amurka da suka shude kan takunkumin tattalin arziki a kan kasashe masu tasowa, a matsayin makamin tsoratarwa da matsin lamba na siyasa, wani lamari ne da ya saba wa muhimman ka’idojin Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya da kuma dokokin kasa da kasa, kuma yana yin zagon kasa ga ginshikin doka da ka’idojin ciniki cikin ‘yanci, kuma yana haifar da keta hakkin bil’adama na asali na al’ummomin da takunkumin ya shafa, musamman ‘yancin ci gaba. Wannan hali sau da yawa yana zama laifi ga ɗan adam.