Leadership News Hausa:
2025-03-28@23:29:26 GMT

‘Yan Fashi Da Makami Sun Kashe Limamin Coci A Gombe

Published: 10th, February 2025 GMT

‘Yan Fashi Da Makami Sun Kashe Limamin Coci A Gombe

Gwamna Inuwa Yahaya, ya kuma umarci hukumomin tsaro da su bi sawun waɗanda suka aikata wannan aika-aika domin kamu su, kana ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin da cocin ECWA, da ɗaukacin al’ummar Kirista, yana mai addu’a ga mamacin.

.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Girgizar ƙasa ta kashe mutum 150 a Myanmar da Thailand

Kimanin mutum 150 ne suka riga mu gidan gaskiya a sanadiyyar wata mummunar girgizar ƙasa daban-daban da suka auku a ƙasashen Myanmar da Thailand.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa girgizar ƙasar wadda ta auku a wannan Juma’ar ta jikkata ɗaruruwan mutane a yayin da baraguzai suka danne gommai.

An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a Zamfara ’Yan sanda sun haramta hawan Sallah a Kano

Hukumar binciken yanayin ƙasa ta Amurka (USGS) ta bayyana cewa an fuskanci wata mummunar girgizar kasa har kashi biyu masu ƙarfin awo 7.7 da 6.4 a Myanmar, tare kuma da wata girgizar ƙasar mai karfi da ta yi ɓarna a kasar Thailand wacce ta shafi wasu wurare a yankin.

Girgizar ƙasa ta farko ta afku ne a wani wuri mai nisan kilomita 16 a arewa maso yammacin birnin Sagaing wacce ta mamayi aƙalla kilomita 10 da misalin ƙarfe 12:50 na daren ƙasar ranar Juma’a, a cewar hukumar binciken yanayin ƙasar ta Amurka USGS.

Gwamnatin ƙasar da za ta gudanar da bincike kan lamarin cikin gaggawa tare da fara ayyukan ceto da kuma samar da kayayyakin agajin jin kai, kamar yadda ta bayyana a shafinta na Telegram.

A cewar wasu shaidu biyu daga garin Taungnoo da ke yankin Bago da suka zanta da kamfanin dillancin labaru na Reuters, aƙalla mutane uku ne suka mutu bayan wani ɓangare na wani masallaci ya rufta.

Girgizar ƙasar ta yi kaca kaca da cibiyar kasuwancin Bangkok haɗi da tituna da gadoji da kuma wani dogon gini mai hawa 30 da ko kammala shi ba a yi ba.

Tuni dai Firaministan Thailand, Paetongtarn Shinawatra ya ayyana dokar ta ɓaci a Bangkok.

Haka kuma, sojojin da ke mulki a Myanmar sun sanar da ayyana dokar ta ɓaci a babban birnin da kuma birni na biyu mafi girma a ƙasar da wasu jihohi shida.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran: Ta’addancin sojojin Amurka a kan Yemen ‘barazana’ ne ga zaman lafiyar duniya
  • Tinubu Ya Ba Da Umarnin Kamo Waɗanda Suka Kashe ‘Yan Arewa A Edo
  • Girgizar ƙasa ta kashe mutum 150 a Myanmar da Thailand
  • Kwankwaso Ya Yi Allah-wadai Da Kisan ‘Yan Arewa A Edo, Ya Buƙaci A Yi Adalci
  • ‘Yansanda Sun Hana Hawan Sallah A Kano Saboda Tsaro
  • An Kama Wanda Ake Zargi Da Kashe Mai PoS A Adamawa
  • Cutar sanƙarau ta yi ajalin mutum 3 a Gombe
  • Miliyoyin  ‘Yahudawa Sun Gudu Neman Mafaka Saboda Makamin Mai Linzami Daga Yemen
  • An kama mutum 3 kan zargin sata da ƙone gidan bature a Gombe
  • ’Yan fashi 4 sun mutu yayin tsere wa ’yan sanda a Nasarawa