Gwamnatin Tarayya Ta Jinjinawa Jihar Jigawa Bisa Kammala Ayyukan Tituna
Published: 10th, February 2025 GMT
Gwamnatin tarayya ta yabawa gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa bisa kammala aikin kaso 97 na ayyukan tituna da ya gada daga gwamnatin da ta gabata a jihar.
Ministan tsaro, Alhaji Badaru Abubakar ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a garin Auyo yayin kaddamar da shirin wayar da kan jama’a da gwamnati da al’umma a jihar Jigawa.
Badaru wanda ya nuna gamsuwarsa matuka, ya ce gwamnatin jihar ta kammala ayyukan tituna guda 23 cikin 26 da ta gada.
Ya kara da cewa sauran ayyukan tituna guda uku sun kusa kammaluwa domin amfanin al’umma da ci gaban tattalin arzikin jihar.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati mai ci za ta kawo karin ayyukan raya kasa, don haka akwai bukatar bai wa gwamnatin jihar duk wani goyon baya da hadin kai don cimma buri da muradin al’umma.
A nasa jawabin Gwamna Umar Namadi ya ce gwamnati mai ci ta zabo sama da makarantu dubu daya da tamanin da za su ci gajiyar shirin bunkasa ilimi tare da hadin gwiwar kungiyar New Globe.
A cewarsa, an zabo makarantun ashirin da biyu a karamar hukumar Auyo da nufin inganta koyo da koyarwa a makarantun gwamnati.
Namadi ya yi nuni da cewa, gwamnatinsa ta bullo da tsare-tsare a karkashin ajandarta guda 12 na samun babban jigawa.
Shi ma da yake jawabi, Sanata mai wakiltar Jigawa ta Arewa maso Yamma, Ambasada Ahmed Abdulhamid Malam Madori ya ce sabon shirin da aka bullo da shi zai kara kusantar da mutane ga gwamnati tare da aiwatar da ayyukan da za su yi tasiri ga rayuwar al’umma.
Gidan rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, bikin ya samu halartar mataimakin gwamnan jihar Injiniya Aminu Usman da kakakin majalisar dokokin jihar Alhaji Haruna Aliyu Dangyatum da sakataren gwamnatin jihar Malam Bala Ibrahim da jami’an gwamnati da kuma ‘yan majalisar dokoki na kasa da na jiha.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano Ta Amince da Kashe Naira Biliyan 33.4 Don Ayyukan Ci Gaba
A wani ɓangare, an ware Naira biliyan 5.22 don gina gidaje 1,000 masu ɗaki biyu-biyu domin raba su kyauta ga waɗanda ambaliya ta shafa. Haka nan, an amince da Naira biliyan 9.76 don gina tituna bakwai da gyaran wasu a karkara