Gwamna Sule ya naɗa Kwamishinoni 16 a Nasarawa
Published: 10th, February 2025 GMT
Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya miƙa wa Majalisar Dokokin jihar sunayen zaɓaɓɓun kwamishinoni 16 domin tabbatarwa.
Shugaban Majalisar, Danladi Jatau ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar da ya gudana ranar Litinin a birnin Lafiya.
Atiku da Obasanjo suna ganawar sirri Ɗalibi ya kashe abokin karatunsu da gatari a NasarawaAminiya ta ruwaito cewa, daga cikin sabbin kwamishinonin da gwamnan ya zaɓa har da tsohon Shugaban Masu Rinjayen a majalisar dokokin jihar, Umar Tanko-Tunga da wani tsohon mamba a majalisar, Mohammed Agah-Muluku.
Kakakin Majalisar ya buƙaci kowane ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun kwamishinonin da su gabatar da kwafi 30 na duk bayanansu daga yanzu zuwa ranar Alhamis tare neman su hallara a gaban majalsiar a ranar Litinin ta makon gobe domin tantance su.
Jerin zaɓaɓɓun kwamishinonin sun haɗa da Yakubu Kwanta daga Ƙaramar Hukumar Akwanga sai Tanko Tunga daga Ƙaramar Hukumar Awe da Munirat Abdullahi da Gabriel Agbashi duk daga Ƙaramar Hukumar Doma.
Akwai kuma Barista Isaac Danladi-Amadu daga Ƙaramar Hukumar Karu da Princess Margret Itaki-Elayo daga Ƙaramar Hukumar Keana da Dokta Ibrahim Tanko daga Ƙaramar Hukumar Keffi LGA da kuma Dokta John DW Mamman daga Ƙaramar Hukumar Kokona.
Sauran sun haɗa da Aminu Mu’azu Maifata da CP Usman Baba mai ritaya daga Ƙaramar Hukumar Lafia. Sai Mohammed Sani-Ottos daga Ƙaramar Hukumar Nasarawa da Mohammed Agah-Muluku daga Ƙaramar Hukumar Nasarawa Eggon da Barista David Moyi daga Ƙaramar Hukumar Obi.
Sai kuma Dokta Gaza Gwamna daga Ƙaramar Hukumar Toto da Barista Judbo Hauwa Samuel da Muazu Gosho duk daga Ƙaramar Hukumar Wamba LGA.
Aminiya ta lura cewa cikin jerin zaɓaɓɓun kwamishinonin 16 akwai tsoffin ’yan majalisar dokokin jihar guda biyu da tsoffin kwamishinoni 6 da kuma mata uku.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Nasarawa Kwamshinoni
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Kaddamar Da Ci Gaba Da Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna
Da yake jawabi a madadin shugaban kasa, Gwamna Uba Sani ya bayyana mahimmancin hanyar wadda ta hada babban birnin tarayya da jihohi sama da 12 dake fadin shiyyar Arewa ta tsakiya, Arewa maso Yamma, da Arewa maso Gabas.
A yayin taron da aka yi a Jere a karamar hukumar Kagarko a ranar Lahadin da ta gabata, Gwamna Sani ya bayyana cewa, an yi biris da aikin hanyar na tsawon shekaru da dama, wanda ya janyo asarar rayuka da kuma illa ga ci gaban tattalin arzikin yankin.
Sai dai Gwamnan ya kafa uzurin cewa, baya ga kudade, rashin tsaro da ake fama da shi a hanyar Kaduna zuwa Abuja a lokacin ne kamfanin Berger ya ki zuwa wurin domin ci gaba da aiki.
Amma a yanzu, hanyoyin da aka bi na magance matsalar tsaro yana haifar da sakamako mai kyau, domin masu ababen hawa na iya bin hanyar ba tare da fargabar an kai musu hari ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp