Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-04-14@18:24:36 GMT

NEMA Ta Bada Tallafi Ga Wadanda Gobara Ta Shafa A Kauran Namoda

Published: 10th, February 2025 GMT

NEMA Ta Bada Tallafi Ga Wadanda Gobara Ta Shafa A Kauran Namoda

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta gabatar da kayan agaji ga gwamnatin jihar Zamfara domin tallafawa wadanda gobara ta shafa a wata makarantar Islamiyya da ke Kaura Namoda.

 

A lokacin da take mika  kayayyakin, Darakta Janar na Hukumar Hajia Zubaida Umar, ta ce matakin ya nuna damuwar gwamnatin tarayya kan halin da wadanda abin ya shafa ke ciki.

Babbar Daraktar wanda shugaban NEMA shiyar Sokoto, Aliyu Shehu Kafindangi ya wakilta, ya ce tallafin ya hada da kayan abinci kamar buhunan shinkafa, da masara, da man girki, da kayayyakin amfani  gida.

A baya dai Hajiya Zubaida Umar ta ziyarci wadanda lamarin ya rutsa da su wadanda har yanzu suke ci gaba da karbar magani a asibitin mata da yara na Khadijah da ke Kaura Namoda.

A asibitin, wakilin na shugabar ta NEMA, ya kuma gabatar da kayayyakin jinya ga hukumar lafiya matakin farko domin ci gaba da kula da wadanda abin ya shafa.

Ya kuma jagoranci tawagar masu ruwa da tsaki da suka hada da wakilan hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Zamfara ZEMA, da  ma’aikatar jin kai ta jihar Zamfara, da kuma karamar hukumar Kaura Namoda zuwa wurin da lamarin ya faru domin jajanta wa makarantar.

Wadanda suka karbi kayayyakin da hukumar ta NEMA ta bayar, a madadin gwamnatin jihar sun hada da babban sakatariyar hukumar ta ZEMA, wadda Daraktan Yaki da iftila’i, Hassan Usman Dauran, da wakilta, da Sarkin Kaura-namoda, Alhaji Sanusi Muhammad Asha da kuma kwamishinan ma’aikatar jin kai ta jihar Zamfara, wanda babban sakataren ma’aikatar  Mohammed Bashir Maradun ya wakilta.

Haka kuma tawagar ta kai ziyarar ban girma ga Sarkin Kaura-namoda, Alhaji Sanusi Muhammad Asha a fadarsa.

Tun da farko, Sarkin Kauran Namoda, Alhaji Sanusi Asha, ya yi alkawarin sanya ido kan rabon kayan abincin ga wadanda abin ya shafa da kwamitin bayar da agajin gaggawa da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi suka kafa.

Hakazalika, ZEMA da ma’aikatar jin kai ta jihar, sun yabawa hukumar NEMA bisa wannan karimcin.

Daga Aminu Dalhatu

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Kauran Namoda jihar Zamfara Kaura Namoda

এছাড়াও পড়ুন:

Yemen Ta Maida Martani Kan Wasu Cibiyoyin Ajiyar Makamai A Yaffa Don Tallafawa Gaza

Sojojin kasar Yemen sun yi amfani da jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa kan cibiyoyin makamai na HKI wadanda suka Yaffa (tel aviv) saboda daukar fansa kan kashe-kashen da take yi a Gaza.

Tashar talabijin Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran YAF na kasar Yemen yana fadar haka a jiya Jumma’a, ya kara da cewa sojojin yahudawan sun kai hare-hare kan unguwar Shaja’iyya inda suka kashe Falasdinawa da dama.

Ya zuwa yanzu tun fara yakin tufanul Aksa, a cikin watan Octoban shekara ta 2023, falasdinawa kimani 51,000 sannan wasu 115,688 a gaza. Ta kuma rusa kimani kasha 90% na gine-ginen Gaza.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Namadi Ya Bada Ai hanyoyi 47 masu nisan kilomita 800 a sassan jihar.
  • ‘Yansanda Sun Kama Wasu Da Ake Zargin Ɓarayin Wayar Wutar Lantarki Ne A Yobe
  • A daina cutar ’yan Najeriya ta hanyar rabon kayan tallafi
  • Hajjin 2025: Shirye-shirye Sun Yi Nisa A Jihar Jigawa
  • Bam Ya Halaka Mutum 8, Ya Jikkata Wasu Da Dama A Borno
  • HKI Ta Jefa Boma-Bomai A Kan Asbiti Tilo Da Ya Rage Yake Aiki A Arewacin Gaza
  • Kallo Daya Mutum Za Yi Min Ya Gane Masana’antar Kannywood Ta Canza Rayuwata -Farida Abdullahi
  • MDD: Mafi Yawancin Wadanda Yaki Ya Ci A Gaza Mata Ne Da Kananan Yara
  • Yemen Ta Maida Martani Kan Wasu Cibiyoyin Ajiyar Makamai A Yaffa Don Tallafawa Gaza
  • Iyaye Mata Sun Bukaci A Rika Samar Da Kayayyakin Bada Tazarar Haihuwa Akan Lokaci