Aminiya:
2025-04-14@18:21:57 GMT

Gwamnan Zamfara ya gindaya sharaɗin sulhu da ’yan bindiga

Published: 10th, February 2025 GMT

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya bayyana cewa sharaɗinsa na sulhu da ’yan bindiga shi ne kawai su daina kashe-kashe su zubar da makamai sannan su miƙa wuya.

A baya dai Gwamna Dare ya sha nanata cewa ba zai yi sulhu da ’yan fashin daji ba.

Gwamna Sule ya naɗa Kwamishinoni 16 a Nasarawa Atiku da Obasanjo suna ganawar sirri

Ko a watan Yulin 2024, sai da wani mai magana da yawunsa, Alhaji Faruk Ahmad, ya bayyana cewa babu wani matsin lamba da zai sa gwamnatinsu ta yi sulhu da ’yan ta’addan.

Ya kuma jaddada cewa mataki ɗaya da gwamnatin ta ɗauka wanda kuma yana haifar da ɗa mai ido shi ne yaƙar ’yan bindigar amma babu batun sulhu.

Sai dai a hirarsa da BBC, Gwamnan ya bayyana cewa ba wai ba za a iya yin sulhu da ’yan bindigar ba ne, “amma ko da za ka yi sulhu ka yi shi a kan gaskiya, ai.

“Akwai da yawa waɗanda aka cutar da su, wasu an kashe iyayensu wasu matansu, saboda haka sai a duba me za a yi masu saboda sun rasa dukiyarsu, bawai kullum a riƙa fitfita ƴanbindiga ba,” in ji Dauda.

Ya ƙara da cewa sai ’yan bindigar sun daina kashe mutane kuma sun ajiye makamansu sannan za a iya yin sulhu da su.

Gwamna Dauda ya bayyana cewa suna samun nasara a yaƙin da suke da ƴanbindiga, “An kashe ’yan ta’adda fiye da 50 a ranar Juma’a a garin Tingar Fulani, wajen Zurmi da Shinkafi.

“Akwai manya-manyan kachalloli da yanzu haka sun tafi lahira, waɗanda suke tare da Bello Turji, akwai Sani Mainasara da Sani Black da Kachallah Auta, Audu Gajere da Kabiru Jangero, Dangajere da makamantansu, duk an hallaka su,” a cewar Dauda Lawal.

Gwamnan ya ce wannan nasara da ake samu za a ci gaba da samunta “har sai na kai ƙarshen lamarin. Ko dai su ajiye makamansu ko kuma mu ba za mu bar su ba.”

Matsin lamba ya sa ’yan bindiga neman sulhu — Makama

Fitaccen mai sharhi kuma masani akan sha’anin tsaro Zagazola Makama ya bayyana cewa matsin lamba da sojoji ke yi wa ’yan bindiga ya sa suke neman sulhu.

Zagazola ya bayyana haka a shafinsa yayin da yake sharhi akan wani faifan bidiyo da yake yawo, inda aka ji Bello Turji da wani shahararren malami a Zamfara, suna tattaunawa akan yadda ɗan bindigar zai ajiye makamai.

A baya-bayan nan, manyan ’yan bindiga da dama sun bayyana aniyarsu ta ajiye makamai sun rungumi zaman lafiya.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Dauda Lawal Dare Jihar Zamfara ya bayyana cewa yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

An kashe mutum kan zargin satar kare a Bauchi 

Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta ce, tana gudanar da bincike kan wani dukan kawo wuƙa da wasu matasa suka yi wa waɗansu mutane su biyu da ake zargi da satar kare a unguwar Lushi da ke cikin garin Bauchi.

Dukan da ya yi sanadin rasa ran ɗaya daga cikinsu mai suna Peter.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya sanar da haka ga manema labarai a Bauchi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Larabar da ta gabata kan wani mutum mai suna Peter a ranar 9 ga Afrilu, 2025, da misalin ƙarfe 11:30 na dare.

An gano gawar makiyayi da ƙwato shanu a Filato An saki fasto an kuma tsare wanda ya kai kuɗin fansa

Wakil ya ce waɗanda ake zargi Dokagk Danladi mai shekara 38 da kuma Peter matasan sun musu duka ne sakamakon zargin da ake musu.

Ya ce, “Dokagk ya samu munanan raunuka da suka haɗa da raunukan sara da adda a kansa, kuma tuni aka kai shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) da ke Bauchi domin kula da lafiyarsa, an gano abokin nasa Peter, wanda har yanzu ba a san sunan babansa ba, a wurin da lamarin ya faru, abin takaici ma’aikatan lafiya sun bayyana cewa shi peter ya mutu.”

A halin yanzu ana gudanar da bincike.  Rundunar tana aiki tuƙuru don ganin an gudanar da cikakken bincike kan wannan lamari, tare da maida hankali wajen zaƙulo duk waɗanda ke da hannu a lamarin.

Wakil ya ce babban Jami’in  ’yan sanda da ke kula da shiyyar Yalwa (DPO) yana jagorantar tawagar masu binciken waɗanda suka ziyarci wurin da laifin da ya faru don tattara shaida da samun cikakken bayanai kan lamarin  .

Kakakin rundunar ’yan sandan ya ce, Kwamishinan ’yan sandan, Sani-Omolori Aliyu ya bayyana wannan aika-aika a matsayin “wata ɓarna da kuma illa ga tsarin dokokin ƙasarmu”.

“Ya kuma gargaɗi ’yan asalin Jihar Bauchi cewa, a ƙarƙashin shugabancinsa rundunar ba za ta lamunci duk wani mutum da ke ɗaukar doka a hannunsu ta hanyar cutar da waɗanda ake zargi da aikata laifukan da suka saɓa wa doka ba.

“Ya ƙara jaddada cewa, babu wani mutum da ke da hurumin mu’amala da wanda ake tuhuma ta hanyar da ba ta dace ba, kuma hakan ba daidai ba ne ga kowa ya ɗauki nauyin aiwatar da doka.  Ya kamata a gaggauta miƙa waɗanda ake zargi da aikata laifin da ake tuhuma ga ‘yan sanda ko hukumomin da abin ya shafa da ke da alhakin bincike da gurfanar da su a gaban kotu.”

Kwamishinan ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu yayin da ake ci gaba da bincike.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan bindiga sun kashe mutane 40 a sabon hari a Filato
  • Hukumar OCHA Ta Bayyana Cewa Yahudawan Sahyoniyya Sun Ninninka Ayyukan Korar Falasdinawa A Yamma Da Kogin Jordan
  • ’Yan bindiga sun kona masallacin Juma’a da asibiti da gidaje da Zamfara
  • Inganta Rayuwar Al’umma: Amurka Da Ƙungiyar Kasuwanci Ta Nijeriya Sun Karrama Gwamna Lawal
  • Ta kai ƙarar kamfanin jirgi da fasinja kan kukan yaro
  • An kashe Uba da ’ya’yansa biyu a ƙauyen Filato
  • An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Gwaska da mayaƙa 100 a Katsina
  • Mutane Da Yawa Sun Jikkata Bayan Fashewar Bam A Wata Kasuwa A Ikeja
  • Kashe-kashen Filato: Jami’an tsaro na sassauta wa masu laifi —Tsohon gwamnan soji
  • An kashe mutum kan zargin satar kare a Bauchi