Xi Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Shugaban Namibia Na Farko
Published: 10th, February 2025 GMT
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon ta’aziyya ga takwaransa na Namibia, Nangolo Mbumba, bisa rasuwar shugaban kasar na farko, Sam Nujoma.
A madadin gwamnati da al’ummar Sinawa, shugaba Xi Jinping ya bayyana jimami tare da yin ta’aziyya ga iyalan Nujoma da ma gwamnati da al’ummar kasar Nambia.
এছাড়াও পড়ুন:
An Yi Taron Tattaunawar Kasa Da Kasa Kan Damammakin Da Sin Ke Gabatarwa A Rasha
Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG ya gabatar da taron tattaunawar kasa da kasa mai taken “Sin a lokacin bazara: More damammakin da take gabatarwa ga duniya” a ran 20 ga watan nan da muke ciki a kasar Rasha. Kuma Shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.
Jakadan Sin dake kasar Rasha, Zhang Hanhui da wakilan bangaren siyasa da ba da ilmi da yada labarai na kasar Rasha sun halarci taron don tattaunawa kan hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen biyu da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da musanyar al’adu da kuma hadin kan kafofin yada labarai da sauransu. Wakilai na Rasha sun hada da Andrey Denisov, mataimakin shugaba na farko na kwamiti mai kula da harkokin ketare na tarayyar kasar Rasha, da kuma Alexander Yakovenko, mataimakin babban manajan rukunin yada labarai na“Rossiya Segodnya”,kana da Andrey Margolin, mataimakin shugaban kwalejin nazarin tattalin arziki da harkokin al’umma dake karkashin shugaban Rasha wato (RANEPA), da Yuri Mazei, mataimakin shugaban jami’ar Lomonosov Moscow, kana da Mikhail Chkanikov, babban editan jaridar “Arguments and Facts”. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp