Leadership News Hausa:
2025-04-16@10:35:11 GMT

Gasar Gajerun Labarun Soyayya Ta LEADERSHIP HAUSA 2025

Published: 10th, February 2025 GMT

Gasar Gajerun Labarun Soyayya Ta LEADERSHIP HAUSA 2025

3. Wallafa labarin a kasan wannan sanarwar a ɓangaren tsokaci.

4. Wallafa labarin a shafinka na sada zumunta na facebook tare da makala #tak na #GasarLabarunSoyayya #LeadershipHausa #GasarLeadership

5. ⁠A kiyaye ƙa’idojin Rubutun Hausa da kuma amfani da daidaitacciyar Hausa da aka amince a yi amfani da ita a hukumance.

6. ⁠Ka tabbatar ka sanya lambar wayarka da sanya adireshinka na Imel a kasan labarin da ka kawo, ka kuma turo mana ta Imel dinmu na: [email protected]

Za a rufe karɓar gajerun labaran a ranar Alhamis mai zuwa 13/02/2025 da karfe 12, na rana.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Dalilin da Kwankwaso zai dawo APC — Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa ƙiris ya rage madugun jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya dawo jam’iyyarsu ta APC.

Gamduje ya bayyana hakan ne yana mai cewa jam’iyyar NNPP ta mutu murus, kuma jana’izarta kaɗai suke jira a gudanar a nan kusa.

Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu ranar Juma’a da Litinin Barcelona da PSG sun tsallaka zagayen kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai

Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin ziyarar da wata ƙungiya mai goyon bayan Shugaba Bola Tinubu (TSG) ta kai sakatariyar APC ta ƙasa da ke Abuja.

Ganduje ya ce APC a kodayaushe tana cikin shirin karɓar jiga-jigan ‘yan siyasa ciki har da Kwankwaso “idan har ya yanke shawarar dawowa gida.”

Ganduje ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP ta rasa duk wani karfi da tasiri da take da shi, musamman a Jihar Kano, inda ya ce ‘yan jam’iyyar da dama sun bar ta.

Ya ce: “NNPP ta mutu. Kuma ba da jimawa ba za a birne ta. Amma abin da ya rage shi ne a haƙa kabari, kuma har an fara hakan. Muna jiran a kammala shiri ne kawai.”

A cewarsa, “Kwankwason ya fara yunƙurin dawowa APC saboda ya fahimci cewa ya rasa komai a jam’iyyar da ya tallata.”

“Ƙofa a buɗe take ga duk wanda ya shirya dawowa APC”, yana mai cewa Kwankwaso zai samu tarba mai kyau idan ya dawo gida.

“Za mu karɓe shi idan ya dawo, domin gida zai dawo,” in ji Ganduje.

Ya ƙara da cewa APC ta na ci gaba da karɓar fitattun ‘yan siyasa daga sassa daban-daban, wanda hakan ke ƙara ƙarfafa jam’iyyar a faɗin ƙasar.

Haɗakar ’yan adawa ba za ta yi tasiri ba — Ganduje

Shugaban jam’iyyar ta APC ya kuma ce haɗakar da wasu ‘yan siyasa ke ƙoƙarin yi domin ƙalubalantar Shugaba Tinubu a Zaɓen 2027 ba za ta yi tasiri ba “domin kuwa rushewa za ta yi kafin a je ko’ina.”

Ganduje ya ce: “Wannan haɗakar da ake ta surutai a kai, za ta tarwatse kafin ta gama haɗuwa. Yawancin su za su dawo cikin APC, domin sun san cewa nan ne gida.”

Ganduje ya jaddada cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da jan ragamar mulki a Nijeriya saboda ingantattun manufofi da kuma salon shugabancin Tinubu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dalilin da Kwankwaso zai dawo APC — Ganduje
  • Barcelona da PSG sun tsallaka zagayen kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai
  • Hajj 2025: Hukumar Alhazai Ta Shirya Taron Bita Ga Mahajjata a Jihar Kwara
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bukaci Jami’an Tsaro Mata Su Rika Sanya Hijabi Yayin Aiki
  • Kotu Ta Tsare Matasa 2 Kan Wallafa Bidiyon Batsa A TikTok A Kano
  • Gwamnatin Kano Za Ta Sake Buɗe Makarantun Kwana 10 Don Inganta Ilimin Yara Mata
  • Kotu ta tsare ’yan TikTok 2 a Kano
  • Gwamna Namadi Ya Bada Ai hanyoyi 47 masu nisan kilomita 800 a sassan jihar.
  • Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya
  • Hajjin 2025: Shirye-shirye Sun Yi Nisa A Jihar Jigawa