Hukumar Sauraran Korafe-Korafe Ta Jigawa Za Ta Kulla Alaka Da Takwararta Ta Abuja
Published: 10th, February 2025 GMT
A kokarinta na karfafa hadin gwiwa da tabbatar da gaskiya da rikon amana, hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Jigawa (JG-PCACC) ta kai ziyarar ban girma ga takwararta da ke Abuja.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulda da jama’a na JG-PCACC Alhaji Yusuf Suleiman ya bai wa gidan rediyon Najeriya a birnin Dutse na jihar Jigawa.
A cewarsa, sun kai ziyarar ce karkashin jagorancin shugaban PCACC, Barista Salisu Abdu, da zummar tantancewa da kuma cudanya da masu ruwa da tsaki a hukumar, tare da lalubo hanyoyin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu.
Barista Salisu Abdu ya jaddada mahimmancin hadin gwiwar t domin hana cin zarafi da rashin adalci a hukumomi da cibiyoyin gwamnati.
“Mun yi imanin cewa ta hanyar yin aiki tare, za mu iya samun ci gaba da samar da ingantacciyar al’umma.
“Ziyarar da muka kawo a yau wata shaida ce da ke nuna aniyarmu ta hada kai da kuma kawar da jihar Jigawa daga kowane irin zalunci.
Barista Abdu ya kuma shaida wa babban kwamishinan cewa hukumarsa na son yin amfani da kwarewar hukumar korafe-korafen jama’a ta fannin horar da ma’aikata.
“Muna da tabbacin hukumarku za ta iya taimaka mana da shawarwari, da horarwa da goyon baya kan mafi kyawun ayyuka wajen tafiyar da koke-koken jama’a duba da nasarorin da kuka samu tsawon shekaru.” In ji Barr. Abdu.
Shugaban ya kuma bayyana cewa JG-PCACC na da ayyuka guda biyu da suka hada da sauraran korafe-korafen jama’a da kuma yaki da cin hanci da rashawa, inda ya ce tun farko hukumar ta karbi korafe-korafe sama da 150 tare da warware su cikin ruwan sanyi.
“Muna da tasiri sosai a fannin korafe-korafen jama’a, tun daga farko mun samu kararraki sama da 150 da suka hada da batutuwan aure, daGado, da karbo basussuka, da takaddamar ciniki, da dai sauransu, kuma da dama daga cikinsu an warwaresu.” In ji shugaban na JGPCACC.
A nasa jawabin, shugaban hukumar kula da korafe-korafen jama’a da ke Abuja (PCC), Bashir Abubakar ya bayyanawa jami’an hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Jigawa irin tasirin da hukumarsa ta ke bi wajen magance rikice-rikice.
“Jihar Jigawa na daya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya amma za ku iya taimakawa jihar wajen samun nasara idan kun yi amfani da fasahar sadarwa ta zamani wajen kawo korafe-korafe cikin sauki,” inji shi.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa korafe korafen jama a korafe korafe jihar Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Uba Sani Ya Nada Sarkin Kauru Amirul Hajj Na Shekarar 2025
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya naɗa Sarkin Kauru, Mai Martaba Alhaji Ya’u Shehu Usman, a matsayin Amirul Hajj kuma jagoran tawagar jami’an jihar don aikin Hajjin 2025.
A cikin wata sanarwa, Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna, Ibraheem Musa, ya bayyana cewa naɗin wannan basarake mai daraja ya biyo bayan sadaukarwarsa, da gaskiya, da jagorancinsa, da nagarta a harkokin mulki.
A matsayinsa na Amirul Hajj, Sarkin zai yi aiki kafada da kafada da Kwamitin Hajj na Musamman na Jihar Kaduna tare da haɗin gwiwa da hukumomin Jiha, Tarayya, da na ƙasashen duniya, domin tabbatar da aikin Hajji cikin nasara ga maniyyatan Jihar Kaduna.
Gwamnan ya kuma yi addu’a ga Allah da ya ma Sarkin jagora da kariya yayin gudanar da wannan muhimmin aiki.
Safiyah Abdulkadir