HOTUNA: Abba ya rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin Kano
Published: 11th, February 2025 GMT
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin Kano, Umar Farouk Ibrahim.
An dai rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin ne a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da aka gudanar ofishin gwamnan.
’Yan bindiga sun kashe fasto a Gombe An shiga nuna wa juna yatsa tsakanin Hamas da Isra’ilaAminiya ta ruwaito cewa, Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Kano, Barista Haruna Isa Dederi ne ya ba shi rantsuwar kama aikin.
Naɗin sabon Sakataren Gwamnatin na zuwa ne watanni biyu bayan sauke Dokta Abdullahi Baffa Bichi daga muƙamin da wasu kwamishinoni 5 da shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnan.
Wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan na Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ce an zaɓi sabon Sakataren Gwamnatin ne saboda ƙwarewar da ya ke da ita, wadda za ta taimaka wajen bunƙasa manufofin da gwamnatin ta Abba Kabir Yusuf ta sa a gaba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Sakataren Gwamnatin Kano Umar Farouq Ibrahim sabon Sakataren Gwamnatin
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Hamas Ta Yi Watsi Da Karin Shuruddan Gwamnatin ‘Yan Sayoniyya Kan Tsagaita Bude Wuta
Kungiyar Hamas ta ki amincewa da sabbin sharuddan fira ministyan gwamnatin mamayar Isra’ila na yarjejeniyar Gaza kashi na biyu
Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu a hukumance ya yanke shawarar fara tattaunawa kan mataki na biyu na yarjejeniyar Gaza, tare da sanya sabbin sharudda. A nata bangaren kungiyar Hamas ta ki amincewa da sharadin ficewarta daga yankin Zirin Gaza da kuma yin fatali da bukatar ajiye makamai a matsayin wani bangare na kowace yarjejeniya.
A yayin da ake fara shirye-shiryen fara gudanar da mataki na biyu na shawarwari tsakanin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da kungiyar Hamas bisa tsarin tsagaita bude wuta da yarjejeniyar musayar fursunoni, gwamnatin yahudawan sahayoniyya yana ci gaba da yin jinkiri ta hanyar kokarin kafa sabbin sharudda, yayin da kungiyar Hamas ta sanar da cewa, ba zata amince da ficewa daga zirin Gaza ko kuma kwance damarar makamanta ba.