Trump : Falasdinawa Ba Su Da Hakkin Komawa Gaza Idan Amurka Ta Kwace Yankin
Published: 11th, February 2025 GMT
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa shirin korar al’ummar Zirin Gaza zai hada da kwace ‘yancinsu na komawa kasarsu.
Trump ya fada a wata hira da tashar Fox News cewa shirin da yake yi a kan Gaza ya kunshi fitar da daukacin al’ummar yankin da kuma sake gina abin da ya kira ‘’Sake farfado da Gabas Ta Tsakiya’’
Ya kara da cewa za a iya samun wurare daban-daban har guda shida don Falasdinawa su zauna a wajen zirin Gaza.
Ya kuma ce za’a gina wa Falasdinawa gidaje masu kyau da inganci nesa da wajen da suke, saidai bai bayyana takamaiman wuri ba.
A wani labarin kuma Donald Trump ya fada a ranar Litinin din nan cewa cewa “watakila” zai daina ba da taimako ga Masar da Jordan idan ba su karbi Falasdinawa daga Gaza ba.
Kasashen biyu dai duk sun yi fatali da shirin na Trump.
Ko a ranar Litinin din masar ta yi watsi da “duk wani sulhu” da ke tauye hakkin Falasdinawa mazauna Gaza, bayan da ministan harkokin wajen kasar ya gana da takwaransa na Amurka a birnin Washington.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ukraine na Fuskantar Wata Barazana, Dangane Da Bukatar Amurka Na Kwace Iko Da Cibiyar Gas Na Rasha A cikin Kasar
Labaran da suke fitowa daga kasar Ukraine sun bayyana cewa, gwamnatin kasar tana son karban iko da bututun iskar gas na kasar Rasha wanda yake yammacin kasar da Turai, wanda kuma yake kai iskar gasa zuwa kasashen Turai.
An gina bututun tun zamanin tarayyar Soviet kuma kasashen biyu suna samun kudade masu yawa daga wannan bututun.
Gwamnatin kasar Amurka dai tana son ta dawo da kudaden da ta kashewa kasar Ukraine na makamai wacce ta karba a likacin shugaban Biden. Daga cikin dai Amurka ta bukaci Ukraine ta bada ma’adinanta na kimani dalar Amurka biliyon $500.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa jami’an gwanatocin kasashen Amurka da Ukraine sun tattauna wannan batun a ranar jumma’an da ta gabata, don tattauna batun irin ma’adinan da kasar Ukraine zasu bawa Amurka saboda biyan kudaden da take binta basgi. Har’ila yau Amurkawan sun gabatar da shawarar kasashen biyu su hada giwa don samun riba tare a aikin hakar Ma’adinan.