HausaTv:
2025-04-15@03:12:16 GMT

Iran Ta Soki Kalaman Netanyahu Na Cewa A Kafa Falasdinu A Saudiyya

Published: 11th, February 2025 GMT

Iran, ta la’anci kalaman foraministan Isra’ila dake cewa a kasa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya.

Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya yi kakkausar suka ga kalaman na Benjamin Netanyahu da ke nuna cewa a kafa kasar Falasdinu a Saudiyya, yana mai danganta hakan da tsokana da kuma barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin.

Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan a ranar Litinin yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan shawarar Amurka da Isra’ila kan Falasdinu.

A yayin tattaunawar shi ma ministan harkokin wajen Saudiyya  ya nuna adawar Saudiyya ta tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga Gaza ko wasu yankunan.

Tunda farko dama kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta yi kakkausar suka kan munanan kalamai da kuma rashin da’a da firaministan Isra’ila ya yi na yin kira da a kafa kasar Falasdinu a kasar Saudiyya.

A ranar Alhamis, ne Netanyahu ya ba da shawara yayin wata hira da tashar 14 ta Isra’ila cewa “Saudiyya za ta iya kafa kasar Falasdinu a Saudiyya, suna da kasa mai girma.”

Kungiyar ta OIC ta dauki wannan a matsayin tsokana ga Saudiyya, kuma cin zarafi ne ga ’yancin kai, tsaron kasa da kuma yankinta, da kuma keta dokokin kasa da kasa da kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kasar Falasdinu a

এছাড়াও পড়ুন:

A Kasar Gabon Brice Oligui Nguema Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa

Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Gabon wanda ya tsaya takarar shugabancin kasar, ya lashe zabe da kawo 90.35% kamar yadda sanarwar ma’aikatar cikin gida ta sanar.

Brice Nguema ne dai ya jagoranci juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin Ali Bango a watan Ogusta na shekarar 2023, ya kuma shiga cikin ‘yan takarar shugabancin kasar a wannan zaben.

Dan takara na biyu da yake binsa a baya, shi ne  Alain Claude Bilie Bie Nze da ya sami kaso 3.02% na jumillar kuri’un da aka kada.

An sami halartar kaso 70.4% na jumillar wadanda su ka cancanci kada kuri’a da ya zama mai muhimmanci  da zai kawo karshen mulkin rikon kwarya na soja.

Zaben na wannan lokacin shi ne irinsa na farko tun 2023.

Yawan masu kada kuri’ar dai sun kai 920,000, sai kuma masu sa idanu daga kasashen waje da sun kai 28,000.

Adadin mutanen kasar Gabon ya kai miliyan 2.3  da mafi yawancinsu suke rayuwar talauci duk da cewa Allah ya huwace wa kasar arzikin man fetur.

Masu Sanya idanu akan zaben sun ce, a kalla san sami kula da dukkanin ka’idojin zabe a cikin kaso 94.8 na mazabun kasar, kuma an baje komai a faifai ba tare da kumbaya-kumbiya ba da kaso 98.6%. Gabanin yin juyin mulkin da ya kawo karshen mulkin iyalan Bango na shekaru 50, Oligui Nguema ya kasance shugaban rundunar da take tsaron fadar shugaban kasa na  kusan shekaru biyu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Kebbi Za Ta Dauki Nauyin Karatun Dalibai A Saudiyya
  • A Kasar Gabon Brice Oligui Nguema Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa
  • Iran Ta Ce Za’a Gudanar Da Zagaye Na Gaba Tsakaninta Da Amurka Ne A Birnin Roma Na Kasar Italiya
  • Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya
  • Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Makiya Suna Hasadan Ci Gaban Kasar Iran
  • Iran Zata Yaye Labulen Ire-Iren Makamanta Na Musamman Da Ta Mallaka Domin Kare Kai
  • Shugaban Burkina Faso Ya Yi Fatali Da Tayin Saudiyya Na Gina Masallatai 200 A Kasarsa
  • Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa na fatan nasara ga tattaunawar Amurka da Iran
  • Isra’ila ta yi barazanar fadada hare-hare Gaza yayin da ta yanke Rafah daga birnin Khan Yunis
  • Ficewar Kasar Nijar Daga Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kasa Da Kasa Barazana Ce Ga Tsaro -Hedikwatar Tsaro