Pezeshkian : Iran Za Ta Dakile Duk Makircin Makiya
Published: 11th, February 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta yi kokarin dakile duk wani makirce-makircen da makiya ke kitsawa.
Shugaban na Iran ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga dimbin jama’a da suka halarci bikin cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a shekara ta 1979 a birnin Tehran yau Litinin.
Shugaba Pezeshkian Ya soki ikirarin shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan na cewa yana son tattaunawa da Iran yayin da a lokaci guda ya ba da umarnin kakaba wa Iran takunkumi kan man da take fitarwa zuwa sifiri.”
Trump ya yi ikirarin cewa Iran na kawo cikas ga tsaron yankin amma “Isra’ila ce, tare da goyon bayan Amurka, tushen duk wani rashin tsaro a yankin da jefa kisan kiyashi a Gaza, hare-hare a kasashen Lebanon, Siriya, Iran da kuma duk inda ta ga dama.”
Pezeshkian ya yi gargadin cewa makiya suna neman haifar da fitina a cikin Iran, Sai dai kuma ba su san cewa a karkashin jagorancin Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei da kuma irin sadaukarwar da al’ummar Iran suke yi, za’a kawo karshen duk wannan mafarki.
Shugaban na Iran ya kara da cewa, Iran ba ta taba neman kaddamar da yaki kan wata kasa ba, kuma ba za ta taba mika wuya ga makiya ba.
Iran ba za ta taba barin makiya su aiwatar da munanan manufofinsu ba, in ji shugaba Pezeshkian.
Ya nanata kudurin Iran na samun zaman lafiya tare da makwabtanta bisa ‘yan uwantaka da mutunta juna, game da batun Gaza kuma, muna kare wadanda ake zalunta ne inji shi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Amurka Ta Yi Da’war Cewa; Ba Ta Neman Tashin Hankali Tsakaninta Da Iran
Gwamnatin Amurka ta sanar da cewa: Ba ta neman tada tashin hankali tsakaninta da Iran
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Samuel Werberg ya bayyana cewa: Kasarsa ba ta neman kara ruruta wutar rikici da Iran, yana mai jaddada cewa har yanzu kofar diflomasiyya a bude take, duk kuwa da kakkausar murya da Amurka ta yi na kin amincewa Iran ta mallaki makamin nukiliya.
Werberg ya kara da cewa; Za su ci gaba da riko da siyasar matsin lamba da nufin dakatar da ci gaba a shirin nukiliyar Iran.
Kakakin na Amurka ya bayyana cewa, “Dole ne Iran ta nuna kyakkyawar niyyarta kafin ta yi magana kan duk wata nasara da za a samu.