Jami’ar Bayero Ta Shirya Bikin Yaye Ɗalibai Karo Na 39
Published: 11th, February 2025 GMT
Jami’ar Bayero Ta Shirya Bikin Yaye Ɗalibai Karo Na 39.
কীওয়ার্ড: Bayero
এছাড়াও পড়ুন:
Ɗaliba ta rasu yayin da gini ya rufta a GGTC Potiskum
Wani ginin ajujuwa a Kwalejin ’Yan Mata ta Kimiyya da Fasaha (GGTC) Potiskum ya rufta, inda daliba ɗaya ta rasu kuma wasu da dama suka jikkata.
Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da ɗalibai ke tsaka da karatu.
An rufe Jami’ar Kogi saboda zanga-zangar ɗalibai EFCC ta gargaɗi ciyamomi kan amfani da kuɗaɗen jama’a a GombeGini ya faɗa kansu ne ba zato ba tsammani, lamarin ya haddasa mummunan tashin hankali tare da jefa ɗalibai da dama cikin baraguzan gini.
Bayan aukuwar lamarin, an yi gaggawar ceto ɗaliban, inda aka garzaya da su zuwa Asibitin Ƙwararru na Potiskum domin ba su kulawa.
Duk da an samu nasarar ceto da dama daga cikinsu, wata ɗaliba ta rasa ranta sakamakon raunukan da ta samu.
Tuni Kwamishinan Ilimi a matakin Farko da Sakandare, Farfesa Abba Idris Adam, tare da Sakataren Zartarwa na Hukumar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Yobe, Dokta Dauda Atiyaye, suka ziyarci wajen da lamarin ya faru, da kuma asibitin da ake kula da ɗaliban da suka jikkata.
Har yanzu ba a bayyana abin da ya yi sanadin rushewar ginin ba.
Amma hukumomi na ci gaba da bincike don gano haƙiƙanin dalilin aukuwar iftila’in.
Garin Potiskum na da nisan kilomita 100 daga Damaturu, Babban Birnin Jihar Yobe.