Trump Ya Yi Wa Falasdinawa Jordan Da Masar Barazana Akan Yankin Gaza
Published: 11th, February 2025 GMT
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar cewa matukar Falasdinawa ba su saki fursunonin Isra’ila ba daga nan zuwa Asabar, to za a kawo karshen tsagaita wutar yakin da aka yi, da komawa yaki.
Shugaban kasar ta Amurka ya shata wa’adin 12: 00 Na ranar Asabar a matsayin lokacin karshe na mika fursunonin.
Shugaban kasar ta Amurka wanda yake Magana da ‘yan jarida a ofis dinsa dake fadar White House, ya sake jaddada tsohuwar barazanar da ya yi tun kafin a rantsar da shi, na ce wa zai bude kofofin jahannama idan ba a mayar da fursunonin ba daga Gaza.”
Donald Trump ya kara da cewa, ya yi Magana da Benjamin Netanyahu akan wa’adin na karshe a ranar Asabar mai zuwa.
Dangane da batun fitar da Falasdinawa daga Gaza kuwa, shugaban kasar ta Amurka ya ce, ya yi imani da cewa Jordan za ta karbi Falasdinawan, tare da barazanar dakatar da taimakon da Amurka take bai wa kasar idan ba ta yi hakan ba.
Ita ma Kasar Masar ta fuskanci barazanar Amurka idan ba ta karbi Falasdinawan da Trump yake tunanin korarsu daga Gaza ba.
Shugaban kasar ta Amurka ya bayyana cewa, zai sayi yankin Gaza domin yin gine-gine na kasuwanci a ciki, lamarin da ya jawo masa mayar da martani daga sassa daban-daban na duniya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Shugaban kasar ta Amurka
এছাড়াও পড়ুন:
Gaza: Sojojin HKI Sun Sake Kai Wa Asibitin “Ma’amadani Hari
Jiragen yakin HKI sun harba makamai masu linzami guda biyu akan ginin asibitin Ma’amadani dake Gaza. Harin ya yi sanadiyyar rushewar wasu bangarori da su ka hada dakunan yin gwaje-gwaje da kantin sayar da magani.
Saboda hare-haren na Isra’ila a wannan asibitin, da akwai gwamman marasa lafiya da suke kwance a kasa a waje, yayin da wasu kuma suke kwance wajen asibiti.
Kungiyar Hamas ta bayyana harin da sojojin HKI su ka kai wa asibitin da cewa wani sabon laifi ne na dabbanci da ‘yan sahayoniyar suka tafka a Gaza.
Haka nan kuma Kungiyar ta Hamas ta zargi Amurka da cewa ita ce take bai wa HKI haske akan tafka laifukan da take yi a Falasdinu.
Bugu da kari kungiyar ta Hamas ta kuma yi mamaki akan yadda kungiyoyin kasa da kasa da su ka hada da MDD suke yin shiru akan laifukan da ake tafkawa da ba su da tamka a wannan zamanin, akan asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya da cutar da marasa lafiya da korarsu daga asibiti zuwa kan tituna.