HKI: Barazana Ba Ta Tasiri Akan Hamas
Published: 11th, February 2025 GMT
Kafafen watsa labarun HKI sun ce; Barazanar da ake yi wa kungiyar Hamas ba ta wani tasiri a gare ta.
Kafafen watsa labarun na HKI suna yin tambaya akan yadda Hamas din take isar da sakwanni a fakaice ga Isra’ila a yayin bikin mika fursunoni da take shiryawa.
Tashar talabijin din ta 12: ta ambaci cewa; A cikin wannan yanayi mai tsanani da ake ciki, ko wane sako ne kungiyar ta Hamas take son isarwa ta hanyar shirya biki a yayin sakin fursunoni?
Shi kuwa mai yi tashar sharhi, Ohad Hamu, ya ce kungiyar ta Hamas ta isar da sako da harshen Hebrew da take mahana da Isra’ilawa, sai kuma turanci da take Magana da gwamnatin Amurka, da hakan yake nufin kin amincewa da shirin Donald Trump.
Ita kuwa tashar talabijin ta 13: cewa ta yi Hamas ta yi watsi da dukkanin sakwannin da Isra’ila take aike mata, kuma ko kadan ba ta damu da barazanar da ake yi ma ta ba.
Har ila yau tashar talabijin ta 12; ta ce, hotonnin da suke fitowa daga Gaza suna nuni da cewa, har yanzu Hamas ce take iko da yankin.
Shi kuma tsohon Fira ministan HKI Ehud Barack cewa ya yi; rashin tsayyar manufa ta gwmanatin Netanyahu ne ya sa har yanzu Hamas din yake ci gaba da iko da Gaza. Ya kuma kara da cewa, ba ta hanyar kashe shugabannin Hamas ne za a kawo karshenta ba, sai dai ta hanyar samar da wadanda za su maye gurbinta.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Haaretz: Sojojin Isra’ila Suna Kan Shirya Kai Wa Gaza Hari Ta Kasa
Jaridar HKI ta “Haaretz” ta buga wani labara da yake cewa, sojojin HKI suna shirin kai wa Gaza gagarumin hari ta kasa bisa cikakken goyon bayan Donald Trump na Amurka.
Jaridar ta kuma ce; Harin na kasa da sojojin za su kai a cikin zirin Gaza,gagarumi ne a karkashin sabon babban hafsan hafsoshin soja Iyal Zamir.
Har ila yau, marubucin rahoton Amos Har’el ya kuma kara da cewa; A wannan karon sun yi imani da cewa gagarumin harin da za su kai wa Gaza zai sa su cimma manufofin da su ka sanya a gaba da aka kasa a cikin tsawon shekara daya da rabi.
Daga cikin wadannan manufofin da ‘yan sahayoniyar suke son cimmawa da akwai rusa makamai da karfin kungiyar Hamas.
Jaridar ta kuma ce a daidai lokacin da ake maganar tattaunawa domin musayar fursunoni, HKI tana shirin sake amfani da karfin soja domin sake shimfida ikonta a cikin Gaza baki daya.
Danagne da rawar da Amurka take takawa a cikin abubuwan da suke faruwa, iyalan fursunoni wadanda suke da takardun zama, ‘yan Isra’ila a lokaci daya kuma Amurkawa, gwamnatin Amurka ba sanar da su cewa, Donald Trump yana cikin shirin bai wa Benjamine Netanyauhu cikakken goyon bayan idan ya zartar da fara kai hare-hare ta kasa akan Gaza. Haka nan kuma an sanar da cewa, ko kadan Trump ba zai yi wa Netanyahu matsin lamba akan dole sai ya koma kan batun musayar fursunoni ba ta ruwan sanyi.