Kasashen Saudiyya Da Iran Sun Ki Amincewa Da Shirin Korar Falasdinawa Daga Kasarsu
Published: 11th, February 2025 GMT
Da marecen jiya Litinin ne aka yi tattaunawa ta wayar tarho a tsakin ministocin harkokin wajen Iran da na Saudiyya akan shirin Donald Trump na korar Falsdinawa daga Gaza,inda kasashen biyu su ka ki amincewa da shi.
Ministan harkokin wajen na Iran Abbas Arakci, da takwaransa na Saudiyya Faysal Bin Farhaan, sun nuna kin amincewarsu da shirin na shugaban kasar Amurka akan mutanen Gaza.
Ministan harkokin wajen Saudiyya Faysal Bin Farhan ya ce, Saudiyya tana da matsaya tabbatacciya da ita ce kin amincewa da duk wani shiri na korar Falasdinawa da karfi daga Gaza zuwa wata kasa.”
Ministan na Saudiyya ya nuna goyon bayansa ga kiran da Iran ta yi na yin taron kungiyar kasashen musulmi domin tattaunawa wannan batu.
A nashi gefen ministan harkokin wajen Iran ya ce; Shirin na Donald Trump na korar Falasdinawa da karfi daga Gaza, ci gaba ne na tsohon shirin ‘yan mulkin mallaka na shafe hakkokin Falasdianwa, tare da yin kira da a dauki matakin fuskantar wannan makarkashiya.
Haka nan kuma minstan harkokin wajen na Iran ya yi tir da furucin Benjemin Netanyahu dake cewa a kafa kasar Falasdinu a cikin Saudiyya, tare da cewa wannan Magana ce ta dagawa da girman kai na ‘yan mamaya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: harkokin wajen
এছাড়াও পড়ুন:
Za mu ɗauko hayar sojojin ƙetare domin horas da dakarun Nijeriya — Badaru
Za a ɗauko hayar ƙwararrun sojoji daga ƙetare domin horar da sojin ƙasar aikin ƙundumbala wajen tunkarar ’yan ta’adda da kuma ƙwato mutanen da aka yi garkuwa da su a Nijeriya.
Ministan Tsaron Nijeriya, Badaru Abubakar ya sanar da haka lokacin ƙaddamar da aikin horar da sojojin 800 a Jaji da ke Jihar Kaduna.
Gaskiyar abin da ake faɗa kan ’yan fim — Samira Sani Mutum 2,000 za su riƙa kamuwa da cutar HIV duk rana a duniya — MDDAbubakar ya ce baya ga horaswar, gwamnati za ta samar wa dakarun kayan aiki na zamani da za su yi amfani da su wajen daƙile matsalolin tsaron da ake samu.
Ministan ya ce a karon farko, sojojin 800 za su ci gajiyar wannan horaswar, yayin da daga bisani wasu 800 kuma su biyo baya.
Badaru ya ce sun ɗauki wannan matakin ne domin tinkarar matsalar ƴan ta’adda waɗanda su ma ke sauya dabaru a kodayaushe.
Kodayake ministan bai sanar da sunayen ƙasashen da za a ɗauka hayar waɗannan zaratan sojojin ba, amma ya ce za a ɗauko su ne daga wasu ƙasashen duniya bakwai.
A zangon farko kaɗai, jimillar sojojin Nijeriya dubu 2 da 400 ne za a fara bai wa horan na musamman, kafin a tsallaka zuwa zango na biyu.
Ministan ya bayyana cewa, ana samun kwanciyar hankali a wasu yankunan ƙasar sakamakon yadda gwamnati ta duƙufa wajen magance matsalar tsaro, inda har ya ba da misali da yankin Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna, yankin da a cewarsa, an samu zaman lafiya a yanzu.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fama da matsalar ’yan bindiga musamman a yankin arewacin Najeriya, inda suke garkuwa da jama’a domin karɓar kuɗin fansa, yayin da a wasu lokuta suke aiwatar da kisa.