An Kashe Adadin Fararen Hular Da Bai Gaza 55 Ba A Arewacin Congo
Published: 11th, February 2025 GMT
Kungiyoyin da suke dauke da makamai sun kashe fararen hular da ba su gaza 55 ba a wani hari da su ka kai wa wasu kauyuka da sansanin ‘yan hijira a Arewacin DRC.
Mahukunta a yankin na Arewacin DRC sun ambaci cewa wasu masu dauke da makamai na kungiyar CODECO sun kai wa wasu kauyuka da suke yankin Djaiba hare-hare a gundumar Ituri a jiya litinin da dare.
Bugu da kari masu dauke da makaman sun kai hari a cikin sansanin ‘yan hijira da suke a cikin wannan yankin kamar yadda shugaban sansanin Antoinnette Nzale ya fadawa manema labaru.
Ita dai kungiyar CODECO gamayya ce ta kungiyoyin da suke dauke da makamai da su ka fito daga kabiluar Landu, manoma. Shekaru 4 da su ka gabata wannan kungiyar ta kai wasu hare-hare da ta kashe mutane 1,800 tare da jikkata wasu 500 a shekarar 2022.
MDD ta ce wannan harin za a iya daukarsa a matsayin laifi akan bil’adama.
Nzake ya ce; sun kai wa dukkanin kauyukan da suke a yankin hari,” sannan ya kara da cewa; Dakarun tabbatar da zaman lafiya na MDD da ake kira; Monusco, tare da sojojin gwamnatin Congo, sun yi kokarin hana hare-hare amma masu dauke da makaman sun fi karfinsu. A watan Satumba da shekarar da ta kare ma, wannan kungiyar ta CODECO ta kai harin da ta kashe mutane 20 a garin Djugu, wanda shi ne garin da ta kai wa hari a wannan Litinin din da ta gabata.
A can gabashin kasar ta Congo ma dai kungiyar M 23 mai samun goyon bayan Rwanda ta kwace iko da garin Goma mai muhimmanci.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hamas Ta Mika Gawawwakin ‘Yan Isra’ila Hudu Ga Kungiyar Red Cross
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta mika gawawwakin mutum hudu ‘yan Isra’ila ga kungiyar agaji ta Red Cross.
Mutanen dai Isra’ila ta kasha su a cikin wadanda Hamas ta yi garkuwa da su lokacin kai hare-hare a Gaza.
Kungiyar agaji ta Red Cross ta nufi wani wuri a Gaza domin karbar gawawwakin ‘yan Isra’ilan hudu da aka shirya mikawa karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta, kamar yadda kafafen yada labaran Isra’ila suka rawaito.
Dakarun na Hamas sun mika gawawwakin a Khan Younis da ke kudancin birnin Gaza.