Leadership News Hausa:
2025-04-15@23:22:20 GMT

Kare Tsaron Kasa Ko Yunkurin Dankwafe Ci Gaban Duniya?

Published: 11th, February 2025 GMT

Kare Tsaron Kasa Ko Yunkurin Dankwafe Ci Gaban Duniya?

Har kullum, na kan ce, ci gaban kasar Sin wata dama ce ba kalubale ba. A matsayin ’yar Afrika, ci gaban kasar Sin daidai yake da ci gaban nahiyar Afrika domin duk wata nasara da ta samu, ba ta kyashin kai wa Afrika, kuma burinta shi ne ta ga nahiyar ta amfana, ta samu ci gaba, kuma al’umma sun kasance cikin walwala.

Kamata ya yi wannan ra’ayi na kasar Sin na neman ganin ci gaban kowa, ya kasance ra’ayin kasashe manya masu son ganin ci gaban duniya, sai dai yayin da ake fafatukar ganin haka, manyan kasashen su ne ke kokarin dankwafe duniya daga samun irin ci gaban da al’umma ke muradi. (Faeza Mustapha)

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun kama ’yan bindiga 12 a Nijar

Rahotanni daga Nijar na cewa dakarun tsaron ƙasar sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda biyu tare da kama ‘yan bindiga 12 a yankunan Dosso da Diffa na ƙasar.

Kafar watsa labarai ta ActuNiger ta ruwaito cewa a Boumba da ke yankin Dosso ne dakarun tsaron ƙasar suka yi nasarar kashe ‘yan ta’adda biyu bayan dakarun da ke sintiri sun yi arangama da ‘yan ta’addan da suka je daga yankin Falmey.

Kotu ta tsare ’yan TikTok 2 a Kano An rantsar da shugabannin ƙananan hukumomi 34 na Katsina

Kazalika ranar Alhamis ne dakarun tsaron ƙasar suka yi nasarar kama ‘yan bindiga 12 a ƙauyen Jagada da ke yankin Diffa.

TRT ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a lokacin da ‘yan bindiga suka kai farmaki a ƙauyen kuma suka fara yi wa mutane ƙwace.

Ana cikin haka ne mutane suka kira dakarun tsaron da ke ƙauyen Kablewa mai maƙwabtaka kuma dakarun suka kai wa mutanen ƙauyen Jagada ɗauki, inda suka yi nasarar kama 12 daga cikin maharan tare da ƙwace bindigogi biyu ƙirar AK47.

Domin ƙarfafa tsaro a ƙauyen da kuma hana ramuwar gayya daga ‘yan bindigar, an samar da ‘yan sintiri na dindindin da suke sun yawo a cikin ƙauyen.

An garzaya da mutane biyun da suka ji rauni a harin asibitin Kablewa inda a yanzu suke samun kulawa.

Har wa yau, dakarun Nijar sun yi nasarar kama mutum biyu masu yi wa ISWAP safarar kayayyaki a yankin Diffa.

Waɗannan nasarorin na zuwa a lokacin da sojin ƙasar ke ƙoƙarin katse hare-haren ‘yan ta’adda da ƙasar ke fama da su.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin Kasuwar Duniya Ce Kuma Dama Ce Ga Kasa Da Kasa
  • ’Yan Najeriya sun koka kan rashin ingancin shinkafar Gwamantin Tarayya
  • Jama’a sun koka kan rashin inganci shinkafar Gwamanti a Kogi
  • Sojoji sun kama ’yan bindiga 12 a Nijar
  • Brice Ologui Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Gaban Da Kashi 90.35% A Jiya Lahadi
  • Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Dakatar Da Matakin Kare-Karen Harajin Fito Kan Hajojin Da Ake Shigarwa Kasar
  • Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Makiya Suna Hasadan Ci Gaban Kasar Iran
  • Iran Zata Yaye Labulen Ire-Iren Makamanta Na Musamman Da Ta Mallaka Domin Kare Kai
  • Ukraine na Fuskantar Wata Barazana, Dangane Da Bukatar Amurka Na Kwace Iko Da Cibiyar Gas Na Rasha  A cikin Kasar
  • Shugaban Burkina Faso Ya Yi Fatali Da Tayin Saudiyya Na Gina Masallatai 200 A Kasarsa