’Yan Wasan Motsa Jiki Na Asiya Sun Yi Murnar Bikin Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiya Ta Sin A Harbin
Published: 12th, February 2025 GMT
An gabatar da bikin mu’ammalar al’adu a jiya Litinin a birnin Harbin da ake wa lakabin “Birnin kankara”, yayin da ake gudanar da gasar wasannin motsa jiki na lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 a birnin. An yi wannan gaggarumin biki ne bisa jigon “bikin sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato bikin bazara karo na farko bayan shigar da shi jerin bukukuwan gargajiya da aka gada daga kaka da kakanni a duniya, wanda ya zo a kan gabar gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya.
’Yan wasan motsa jiki 20 daga kasar Mongoliya da Thailand da Philipphines da Vietnam da Indiya da Nepal da dai sauran wakilan tawagogin wasannin motsa jiki da ’yan jarida sun yi murnar bikin bazara tare, a dakin watsa labarai na CMG, a bikin baje kolin kayayyakin kankara dake Harbin bayan sun fafata a gasanni daban-daban. (Amina Xu)
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Yaffa Kusa Da Tel Aviv A Karo Na Biyu A Cikin Sa’o’i 24
Sojojin kasar Yemen sun cilla makami mai linzami samfurai Balistic kuma Hypersonic kan birnin Yafa kusa da Telaviv a cikin HKI karo na biyu a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata. Harin dai yana daga cikin manya-manyan hare-haren da sojojin na Yemen suka kai kan HKI tun bayan sake komawa yaki tufanul Aksa.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar ta Yemen Burgediya Janar Yahya Saree yana bada sanarwan kai harin, a jiya Alhamis ya kuma kara da cewa, hari mai kyua wanda ya dace da tallafawa Falasdinawa a Gaza.
Saree ya kammala da cewa matukar sojojin HKI sun ci gaba da kissan kiyashin da suke yi a Gaza