Ba Za a Iya Dakile Rarrabuwar Iko Tsakanin Kasashen Duniya Ba
Published: 12th, February 2025 GMT
Yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun ya gudanar da taron manema labarai da aka saba yi yau da kullum, inda ya yi tsokaci game da rahoton dake da alaka da rarrabuwar iko tsakanin kasashen duniya na taron tsaro na Munich, yana cewa, bisa binciken da taron ya yi, kasa da kasa sun kara amincewa da kasancewar iko tsakanin kasashe daban daban a duniya.
Da ya tabo batun sanya na’urar Buoy da Sin ta yi cikin ruwa don duba yanayin cikin tekun da batun ya shafa, Guo Jiakun ya bayyana cewa, wannan ya dace da dokokin cikin gida na kasar Sin da kuma dokokin kasa da kasa.
Guo Jiakun ya kuma kara da cewa, kasar Sin ta kasance mai kwazo da himma wajen tunkarar sauyin yanayi, kuma za ta cika alkawarinta na cimma burin “daidaita abubuwa masu dumama yanayi da rage fitar da su” bisa hanyoyin da ta zaba. (Safiyah Ma)
এছাড়াও পড়ুন:
An Gudanar Da Taron Karawa Juna Sani Kan Karfafa Rawar Da MDD Ke Takawa A Beijing
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun ya ce a jiya Litinin, ma’aikatar harkokin wajen Sin ta gudanar da taron karawa juna sani na kasa da kasa, mai taken “Karfafa rawar da MDD ke takawa, tare da habaka ra’ayin cudanyar bangarori daban daban” a nan birnin Beijing.
Guo ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na yau da kullum da ya jagoranta a yau Talata, inda ya ce daukacin mahalarta taron na karawa juna sani sun yi imanin cewa, a halin da ake ciki, ya kamata a karfafa ayyukan MDD, da inganta hadin kai da hadin gwiwa, da kuma tinkarar kalubale daban daban da ake fuskanta a duniya. Kazalika, mahalarta taron sun jinjinawa rawar da kasar Sin ta taka a wannan fanni.
Dangane da taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar raya kasar Sin na shekarr 2025 da aka gudanar a nan birnin Beijing kwanan baya, Guo Jiakun ya bayyana cewa, taron shekara-shekarar na bana, ya samu halartar wakilan kasashen wajen sama da 750, kuma kamfanonin da suka halarci taron sun fito ne daga kasashe daban-daban, lamarin da ya nuna cewa, kamfanonin kasashen waje suna da kwarin gwiwar yin kasuwanci da Sin.
Game da rahoto mai taken “Hukumomin leken asiri na Amurka suna sa ido da satar bayanai da suka shafi tashoshin wayar salula na duniya”, wanda kawancen kamfanonin tsaro na Intanet na kasar Sin ya fitar a yau, Guo Jiakun ya ce, kasar Sin ta nuna matukar damuwa game da munanan ayyukan da Amurka ke yi a yanar gizo da aka bayyana a cikin rahoton, ya kuma bukaci Amurka da ta gaggauta dakatar da hakan. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp