An yi wa kashi 25 na matan Nijeriya kaciya
Published: 12th, February 2025 GMT
Masu fafutikar kare haƙƙin bil Adama da ƙwararru a fannin kiwon lafiya haɗi da fasihai a ɓangaren shari’a sun buƙaci a tsananta hukunci kan masu yi wa mata kaciya a Nijeriya.
Masu ruwa da tsakin sun yi kira da a ƙara wayar da kan al’umma domin ganin an daƙile kaciyar mata gaba ɗaya a ƙasar nan.
Garkuwa da Mutane: An kama ɗan shekara 13 a wurin rajistar layin waya DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar HausaA yayin wani taro da aka gudanar kan kawo ƙarshen kaciyar mata a Nijeriya, Nora Agbakhamen, wanda ta assasa Pulse Narrative, ta ce fiye da mata miliyan 200 a faɗin duniya sun fuskanci wani nau’i na kaciya, lamarin da ya shafi kashi 25 cikin 100 na matan Nijeriya.
Agbakhamen ta ce duk da cewa dokokin ƙasa da ƙasa sun ayyyana kaciyar mata a matsayin wani nau’i na cin zarafi da keta haddi, har yanzu matsalar na ci gaba da ta’azzara a sakamakon rashin tsananta hukunci.
A cewarta, akwai buƙatar a haɗa kai da duk masu ruwa da tsaki musamman tare da ƙwararru a fannin kiwon domin wayar da kan al’umma wajen ganin an kawo ƙarshen wannan matsalar.
Mohammed Abubakar na Masarautar Chokalin Fika da ke Jihar Yobe, ya ce sarakunan gargajiya tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyi masu zaman kansu na ci gaba da wayar da kan al’ummominsu kan illolin da ke tattare da kaciyar mata.
Ya bayyana cewa Gwamnatin Yobe ta shimfiɗa dokoki masu tsanani kan masu yi wa mata kaciya domin ganin an shawo kan matsalar.
Yayin da yake bayyana rawar da sarakunan gargajiya suke takawa, ya buƙaci ƙarin haɗin gwiwa domin tunkarar wannan annoba ta hanyar wayar da kan al’umma da shimfiɗa dokoki masu tsanani.
Wata ma’aikaciyar jinya kuma mai fafutikar yaƙi da cin zarafin mata, Amina Waziri Abdullahi, ta bayyana kaciyar mata a matsayin wani nau’i na cin zarafi da yake da mummunan tasiri ga rayuwar mace.
Shi ma wani wani lauya kuma mai fafutikar kare haƙƙin mata, Kowoabi Takoni, ya buƙaci a sanya haddin da ya zarce Naira dubu 200 da a yanzu ake karɓa a wurin waɗanda aka kama da laifin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: cin zarafi Kaciyar Mata kaciyar mata
এছাড়াও পড়ুন:
MDD: Mafi Yawancin Wadanda Yaki Ya Ci A Gaza Mata Ne Da Kananan Yara
Hukumar da take kula da hakkin bil’adama ta MDD ta bayyana cewa; Mafi yawancin wadanda yaki ya rutsa da su a Gaza mata ne da kananan yara.
Mai Magana da yawun hukumar ta kare hakkin bil’adama ta MDD Rafina Shamdsani ce ta bayyana hakan a wurin taron hukumar da aka yi a birnin Geneva tana mai kara da cewa; Atsakanin watan Maris zuwa Aprilu na wannan shekara ta 20205 da ake ciki kadan, Isra’ila ta kai hare-hare har sau 224 akan gidajen mutane da kuma hemomin da ‘yan hijira suke ciki.
Har ila yau, hukumar ta kara da cewa; suna ci gaba gudanar da bincike akan wasu hare-hare 36 da sojojin Isra’ilan su ka kai da aka tabbatar da ya ci rayukan mutane da dama da su ka hada mata da kananan yara.
A nata gefen, kungiyar agaji ta “Red- Cross” ta yi gargadin cewa, kayan aikin da ake da su a cikin asibitocin da ake da su a cikin yankin sun kusa karewa.
Haka nan kuma kungiyar ta ce; ” A cikin yankuna da dama na Gaza, ba a iya samun ruwan sha, babu abinci, kuma babu wutar lantarki.
Ita kuwa ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza, ta yi kiran gaggawa domin a shigar da kayan aiki a cikin asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya. Haka nan kuma ta kara da cewa, da akwai masu fama da ciwon suga 80,000 sai masu hawan jini 110,000 ba su samun kula yadda ya dace.