Kungiyar Tarayyar Afirka Ta Ce: Sudan Ce Kasar Mafi Fama Da Matsalar Jin Kai A Duniya
Published: 12th, February 2025 GMT
Kungiyar Tarayyar Afirka ta bayyana cewa: Sudan ce kasar da aka fi fama da matsalar jin kai a duniya
A zaman tattaunawa da Kungiyar Tarayyar Afirka ta gudanar ta bayyana yakin basasar Sudan a matsayin “mafi girman matsalar jin kai a duniya,” inda ta yi gargadin irin mummunar illar da yake yi kan fararen hula, musamman kananan yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki.
Wadannan kalamai sun zo ne a yayin wani taron tattaunawa da kungiyar Tarayyar Afirka ta gudanar, inda aka yi karin haske kan rikicin da ake yi tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa, wanda ya yi sanadiyyar raba mutane kimanin miliyan 12 da matsugunan su.
Yakin dai ya kawo cikas wajen kai agajin jin kai, ya haifar da karancin abinci da kuma ta’azzara yunwa, in ji Mohamed Ibn Chambas, shugaban kwamitin Tarayyar Afirka kan Sudan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Dakarun Kai Daukin Gaggawa Sun Kashe Mutane Fiye Da 400 A Yankin Al-Qatana Da Ke Jihar White Nile Ta Sudan
‘Yan tawayen Sudan na Dakarun Kai Daukin Gaggawa sun aikata muggan laifuffuka a yankin Al-Qatana da ke Jihar White Nile ta Sudan
Rahotonni sun bayyana cewa: Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan fararen hula a birnin Al-Qatana da ke arewacin jihar White Nile a Sudan, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan fararen hula tare da tarwatsa al’ummar yankin, inda suka fantsama zuwa gudun hijira.
Ma’aikatar harkokin wajen Sudan ta tabbatar da cewa: Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun gudanar da wani kisan kiyashi da ya yi sanadin mutuwar mutane 433 a kauyukan birnin Al-Qatana na jihar White Nile.
Ma’aikatar harkokin wajen Sudan a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce: Dakarun kai daukin gaggawa sun yi amfani da salon da suka saba yi na daukar fansa kan fararen hula da ba su dauke da makamai a kauyuka da kananan garuruwa bayan da suka sha kashi a hannun sojojin Sudan.