Wakilin LEADERSHIP Hausa Ya Zama Shugaban Wakilan Kafafen Yaɗa Labarai A Kebbi
Published: 12th, February 2025 GMT
Wakilin LEADERSHIP Hausa Ya Zama Shugaban Wakilan Kafafen Yaɗa Labarai A Kebbi.
এছাড়াও পড়ুন:
Basukan Da Nijeriya Ke Biya Sun Karu Zuwa Naira Tiriliyan 13
Kudin biyan bashin cikin gida na shekarar 2024 ya kai naira tiriliyan 5.97, wanda hakan ke nuna karin kashi 14.15 cikin 100 daga naira tiriliyan 5.23 da aka samu a shekarar 2023. Karuwar ana danganta shi da karuwar kudin ruwa da karin lamuni na cikin gida.
Nijeriya dai ta kashe dala biliyan 4.66 (kwatankwacin naira tiriliyan 7.15 kan farashin canjin naira 1,535.32/$1), wanda hakan ya nuna karuwar kashi 167 cikin 100 daga naira tiriliyan 2.57 da aka samu a shekarar 2023.
Yawan kudin biyan basussuka na waje yana da nasaba da hauhawar farashin ruwa a duniya da kuma faduwar darajar naira, lamarin da ya sa bashin dala ya yi tsada wajen aiki.
Duk da yawan kudin basukan da ke kan Nijeriya, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da ciwo basuka kadan ta yi amfani da su cikin hanyoyin da suka dace.
Shettima ya bayyana haka ne a karshen makon da ya gabata a Abuja, yayin wani taron da kungiyar akanta ta kasa ta kasa da kuma cibiyar harajin ta Nijeriya ta shirya.
Mataimakin shugaban kasar, wanda ya samu wakilcin mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin tattalin arziki, Dakta Tope Fasua, ya bayyana cewa sannu a hankali ana sake fasalin tsarin karbar basussukan da gwamnati ke yi domin rage bashin.
Ya kuma bayyana cewa, duk da rancen da aka karbo a baya-bayan nan da ya jawo cece-kuce, yanzu Nijeriya na kan hanyar karbar rancen kadan tare da kokarin rage gibin kasafin kudaden da ake fuskanta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp