Aljeriya Ta Yi Maraba Da Shirin Iran Na Gudanar Da Taron OIC Kan Gaza
Published: 12th, February 2025 GMT
Kasar Aljeriya ta yi marhabin da shirin Iran na gudanar da taron kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a zirin Gaza, wanda shugaban na Amurka ya ce yana son karbe iko tare da raba al’ummar kasar baki daya.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya gabatar da shawarar gudanar da wani zama na musamman na kungiyar OIC a ranar Litinin yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Aljeriya Ahmed Attaf, a wani bangare na tuntubar da yake yi da ministocin harkokin wajen kasashen musulmi kan Gaza.
A yayin tattaunawar tasa, Mista Araghchi ya yi cikakken bayani kan shawarwarin da ya yi a baya-bayan nan da shugabannin kasashen musulmi, da kuma babban sakataren kungiyar OIC, Hussein Ibrahim Taha, da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, don jawo hankalin al’ummar duniya kan “makircin tsarkake kabilanci a Gaza”.
Shugaban diflomasiyyar na Iran ya yi maraba da matakin da Aljeriya ta dauka na nuna goyon baya ga tsayin daka da al’ummar Palastinu suke yi na ‘yantar da kansu daga mamayar Isra’ila.
A makon da ya gabata, Trump ya ce Amurka na neman “karbe” Gaza a wani bangare na shirin da ya gabatar a karkashin sunan “sake gina” yankin Falasdinawa da yaki ya daidaita, inda ya ba da shawarar tilastawa wasu ‘yan Gazan miliyan 2.4 gudun hijira zuwa Masar da Jordan.
Tuni dai Alkahira da Amman suka yi watsi da shirin na Trump na tunzura jama’a.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sarkin Qatar Zai Zayarci Tehran A Gobe Laraba
Sarkin Qatar Tamim bin Hamad Al-Thani zai fara ziyarar aiki na kwana guda a nan Tehran, don tattauna al-amura masu muhimmanci da Jami’an gwamnati JMI.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbass Aragchi ya bayyana cewa, a gobe muna tare da sarkin Qatar Tamim bin Hamad Athani, inda zamu tattauna al-amura masu muhimmanci a tsakanin kasashen biyu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar cewa kasar Qatar ta taka rawa a tsagaita wuta tsakanin HKI da kuma kungiyar Hamas, sannan tana da dangantaka mai karfi da kasar Iran.
Ya ce yankin gabasa ta tsakiya tana fuskantar sauye-sauye masu yawa, da kuma barazana iri-iri, kuma wannan zuwan zai kasance sabonta dangantaka tsakanin kasashen biyu ne.
Duk da cewa Aragchi bai bayyana agendar tattaunawar kasashen biyu ba, amma akwai, zaton kasashen biyu zasu tattauna kan sauye-sauyen da ke faruwa a gabas ta tsakiya.