Iran Ta Yi Allah Wadai Da Barazanar Da Trump Ya Yi Mata
Published: 12th, February 2025 GMT
Iran ta yi kakkausar suka kan barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na yin amfani da karfi a kan kasar, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana da rashin da’a.
A cikin wata wasika da ya aike a wannan Talata zuwa ga shugaban Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhu na dindindin jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saïd Iravani, ya bayyana cewa kalaman na Trump na tada hankali sun sabawa dokokin kasa da kasa da kuma kundin tsarin mulkin MDD.
Trump ya ce zai gwammace ya kulla yarjejeniya da Iran maimakon “harba mata bam fiye da kima,” a wata hira da manema labarai a ranar Asabar.
“Na fi son kulla yarjejeniya da ba za ta cutar da su ba,” in ji shi. “Zan so in yi yarjejeniya da su ba tare da kai musu harin bam ba,” in ji Trump ga jaridar New York Post.
Iravani ya bayyana cewa, kalaman na Trump masu hadari da tayar da hankali sun sabawa dokokin kasa da kasa da kuma Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya, musamman a shafi na 2 (4), wanda ya haramta barazana ko amfani da karfi kan kasashe masu cin gashin kai. »
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Nijar Na Son Kulla Yarjejeniya Kafofin Yada Labarai Na Iran
Nijar ta bayyan fatanta na ganin ta kulla yarjejeniya da kafofin yada labarai na Iran.
Wannan bayanin na kunshe ne a bayyannin da jakadan Nijar a Tehran Malam Seydou Ali Zataou, ya yi a ganawarsa da shugaban hukumar gidan radiyo da talabijin sashen kasashen waje na Iran, Ahmad Norozi a wannan Litinin.
Bangarorin sun bayyana kyakyawan fatan musayar bayanai da shirye shirye a tsakaninsu da nufin karya laggon kafofin yada labarai na kasashen yamma dake yada gurbatattun bayanai da rahotanni kan kasashen.
jakadan na NIjar, ya kuma yi tinu da irin kyakyawar alakar dake tsakanin kasashen biyu.