N50,000 aka biya ni don safara harsasai zuwa Abuja – Matashj
Published: 12th, February 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato, ta kama wani matashi tare da wasu mutum uku kan zargin safarar harsasai daga Jos zuwa Abuja.
Matashin ya bayyana cewa ’yan ta’adda sun biya shi Naira 50,000 domin ya karɓo harsasai daga Jos zuwa Abuja.
Majalisa na neman rushe ƙudirin ƙara kuɗin kira da data Noman rani ne zai kawar da yunwa a Yankin Tafkin Chadi — Zulum“Ni mazaunin Abuja ne.
“Ya tabbatar min babu wata matsala da zan fuskanta, amma a hanya jami’an tsaro suka kama mu ni da wasu mutum uku,” in ji matashin.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, yayin da yake holen waɗanda ake zargi, ya ce an kama su ne bayan samun rahoton sirri kan ayyukansu.
“Mun kama waɗanda ake zargin ne bayan samun sahihan bayanan sirri.
“Rundunar na ci gaba da bincike, kuma da zarar an kammala, za a miƙa su zuwa kotu domin fuskantar hukunci.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Harsasai Masu Safarar Makamai matsalar matsalar tsaro Safara
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar M-23 Ta Kasar Kongo Ta Kara Nusawa Gaba A Don Mamaye Karin Yankuna A Gabacin Kongo
Yan tawayen M-23 na kasar Kongo wadanda suke samun goyon bayan gwamnatin kasar Ruwanda sun kara nosawa zuwa gaba a mamayar da sukewa gabancin kasar ta Kongo.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa yan tawayen sun kama garin Walikale a jiya Laraba kuma a halin yanzun sun kokarin zuwa sauran garuruwa a yankin.
Labarin ya kara da cewa wannan labarin na zuwa ne a dai dai lokacinda shuwagabanninkasashen Kongo da Rwanda suke kira ga bangarorin biyu su tsagaita budewa juna wuta su kuma dawo kan teburin tattaunawa.
Wani mazaunin garin walikale ya fadawa reuters yana jin karar bindigogi a garin Nyabangi wanda yake kusa da inda yake.
Janvier Kabutwa yace, yan tawayen sun afafatawa da sojojin Gwamnati da kuma sojojin sa kai a garin bayan da mayakan M-23 suka tunkari sansanin sojojin gwamnati a garin.