NAFDAC Ta Rufe Shaguna Da Wuraren Ajiyar Magunguna Marasa Inganci A Legas.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

 Rasha Ta Sanar Da Kakkabo Da Jirage Marasa Matuki 57 Da Ukiraniya Ta Harba

Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuki 57 da kasar Ukiraniya ta harba zuwa yankuna mabanbanta na kasar.

A yau Laraba ne ma’aikatar tsaron kasar ta Rasha ta sanar da cewa; An harbo jiragen marasa matuki 35 da aka harba wa yankin Kursk dake yammacin Syria a jiya da dare. Sai kuma wasu jiragen 13 da aka harba a yankin Oryol da kuma wasu 7 a samaniyar tekun Azorf. Sauran yankunan da sojojin Ukuraniya su ka harba wa makamai masu linzamin sun hada  Tola, da Biryansk.

Kwanaki biyu da su ka gabaa ma dai sojojin na Rasha sun sanar da kakkabo wasu jirage marasa matuki na Kasar Ukiraniya 31 da aka harba a yankuna mabanbanta na kasar.

 A gefe daya sojojin na kasar Ukiraniya sun kai wasu hare-hare akan garuruwan da suke kan iyaka da Rasha, da su ka hada garuruwan Zawalishnika da Korsta.

Majiyar  tsaron Rasha ta ce, sun kashe sojojin Ukiraniya 220 a cikin sa’oi 24.

A gefe daya Amurka ta sanar da cewa a ranar Lahadi mai zuwa za a bude tattaunawa a tsakanin Rasha da Amurka a birnin Jidda na kasar Saudiyya.

Manzon musamman na Amurka Steve Vitcov ya bayyana cewa,tattaunawar za ta mayar da hankali ne akan yadda za a kawo karshen yakin kasar Ukiraniya.

A jiya Talata an yi tattaunawa ta wayar tarho a tsakanin shugabannin kasashen Rasha da na Amurka akan batun kasar ta Ukiraniya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Rasha Ta Sanar Da Kakkabo Da Jirage Marasa Matuki 57 Da Ukiraniya Ta Harba
  • Shugaban Kasar Sin Ya Jaddada Muhimmancin Nacewa Ga Samun Ci Gaba Mai Inganci Yayin Ziyararsa A Guizhou
  • Gwamna Yusuf Ya Yi Barazanar Ƙwace Lasisin Jerin Gidajen Kwankwasiyya, Amana Da Bandirawo 
  • Tsohon Ɗan Takarar Gwamna A Legas  Ya Koma APC Daga PDP