Zanga-zanga ta ɓarke kan hare-haren ’yan bindiga a Kaduna
Published: 12th, February 2025 GMT
Mazauna Ungwan Ate da ke Ƙaramar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna, sun fito kan tituna domin yin zanga-zanga kan yawaitar hare-haren ’yan bindiga da satar jama’a da suka addabi yankinsu.
Masu zanga-zangar sun toshe hanyar Ungwan Ate zuwa Ungwan Mission da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Kachia.
Ɗan majalisar Kebbi ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC N50,000 aka biya ni don safarar harsasai zuwa Abuja – MatashiSun kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa don kare rayukansu da dukiyoyinsu.
Wani daga cikin masu zanga-zangar da ya zanta da Aminiya, ya ce ’yan bindiga sun shiga Ungwan Ate a daren ranar Talata, inda suka shafe sama da sa’o’i biyu suna cin karensu ba babbaka, tare da sace mutum ɗaya daga ƙauyen.
“Ba mu da kwanciyar hankali kwata-kwata.
“’Yan bindiga suna yawan kawo mana hari a duk lokacin da suka ga dama. Gwamnati da hukumomin tsaro su gaggauta ɗaukar mataki kafin mu ƙare,” in ji shi.
Wani mazaunin yankin ya ce matsalar tsaro a Kachia ta kai ga mutane ba sa iya zuwa gonakinsu ko barci cikin kwanciyar hankali.
“Gwamnati ta ce ta yi sulhu da ‘yan bindiga, amma kullum ana kashe mu a Kachia.
“Mutane da dama na cikin daji suna shan wahala kan laifukan da ba su san komai a kansu ba,” in ji shi cikin fushi.
Masu zanga-zangar sun ce ’yan bindiga sun mayar da yankin filin daga, lamarin da ya sa suka tsinci kansu cikin tsananin fargaba da damuwa.
“Ba ma iya zuwa gona, alhali yawancinmu da noma muka dogara,” in ji wani daga cikin masu zanga-zangar.
“Ba ma iya yin barci cikin kwanciyar hankali. Ana so a ƙarar da mu ne?”
Zanga-zangar ta biyo bayan hare-hare da yawaitar sace-sacen mutane a Ƙaramar Hukumar Kachia.
Ƙauyuka irin su Gadanji, Ungwan Wage, Ungwan Alhaji, Agunu Dutse, Maro da Ungwan Dauje na fama da hare-haren ’yan bindiga ba dare ba rana.
Mazauna yankin sun ce duk da kiraye-kirayen da suke yi ga mahukunta, babu wani matakin tsaro da aka ɗauka domin kare su daga hare-haren.
A halin da ake ciki, mazauna yankin na ci gaba da roƙon gwamnati da hukumomin tsaro da su kawo musu ɗauki domin dawo da zaman lafiya da tsaro a yankin.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, bai amsa kiran waya ba.
Ga hotunan yadda zanga-zangar ta gudana:
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga hare hare Tsaro zanga zangar yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Fiye Da Dalibai 4,200 Suka Amfana Da Tallafin Ilimi Na Sanata Solomon Adeola
Ya kara bayanin cewa an dauki matakin ne inda har abin ya shafi daliban da suke mazabun majalisar Dattawa biyu na Jihar Osun.
Ya nuna jin dadinsa inda ya furta ce wa“Wani abin farinciki ne gare ni dana samu yawan daliban da suka samu damar yin rajista daga mazaba ta da kuma saiuran mazabun na majalisar Dattawa, wadanda su basu samu damar rubuta jarabawar da zata basu damar zuwa manyan makarantu ba a fadin tarayyar Nijeriya.
“Ilimi shi ne wani babban abinda ya kamata kowane dan/ ‘yar kasa su kasance sun samu damar yin haka ta samun sa, don haka lamarain kudi bai dace ace ya hana su damar samun hakan ba musamman ma ga matasa wadanda sune manyan gobe kamar yadda Sanatan ya bayyana”.
Daga karshe ya yi karin bayani ne na shit sarin bada fom domin cikawa saboda rubuta JAMB wata dama ce ita ma tayi kama ko daya take da damar bada guraben karatu zuwa manyan makarantu, na dalibai 500 za a cimma burin yin haka cikin makonni masu zuwa na gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp