Amurka Ba Za Ta Cimma Burinta Bisa Matakin Kara Harajin Kwastam Kan Ma’adanan Karfe Da Goran Ruwa Ba
Published: 12th, February 2025 GMT
Amurka Ba Za Ta Cimma Burinta Bisa Matakin Kara Harajin Kwastam Kan Ma’adanan Karfe Da Goran Ruwa Ba.
এছাড়াও পড়ুন:
MDD: Mafi Yawancin Wadanda Yaki Ya Ci A Gaza Mata Ne Da Kananan Yara
Hukumar da take kula da hakkin bil’adama ta MDD ta bayyana cewa; Mafi yawancin wadanda yaki ya rutsa da su a Gaza mata ne da kananan yara.
Mai Magana da yawun hukumar ta kare hakkin bil’adama ta MDD Rafina Shamdsani ce ta bayyana hakan a wurin taron hukumar da aka yi a birnin Geneva tana mai kara da cewa; Atsakanin watan Maris zuwa Aprilu na wannan shekara ta 20205 da ake ciki kadan, Isra’ila ta kai hare-hare har sau 224 akan gidajen mutane da kuma hemomin da ‘yan hijira suke ciki.
Har ila yau, hukumar ta kara da cewa; suna ci gaba gudanar da bincike akan wasu hare-hare 36 da sojojin Isra’ilan su ka kai da aka tabbatar da ya ci rayukan mutane da dama da su ka hada mata da kananan yara.
A nata gefen, kungiyar agaji ta “Red- Cross” ta yi gargadin cewa, kayan aikin da ake da su a cikin asibitocin da ake da su a cikin yankin sun kusa karewa.
Haka nan kuma kungiyar ta ce; ” A cikin yankuna da dama na Gaza, ba a iya samun ruwan sha, babu abinci, kuma babu wutar lantarki.
Ita kuwa ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza, ta yi kiran gaggawa domin a shigar da kayan aiki a cikin asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya. Haka nan kuma ta kara da cewa, da akwai masu fama da ciwon suga 80,000 sai masu hawan jini 110,000 ba su samun kula yadda ya dace.