Kungiyar Hamas Ta Godewa Kasashen Duniya Wadanda Suka Ki Amincewa Da Shirin Trump Na Korarsu Daga Gaza
Published: 12th, February 2025 GMT
Kungiyar Hamas a Gaza ta godewa kasashen duniya musamman kasashen Jordan da Masar dangane da kin amincewarsu da korar Falasdinawa a Gaza.
Kafin haka dai shugaban kasar Amurka Donal Trump ya ce zai kwace zirin Gaza daga hannun Falasdinawa, sannan zai tsugunar da su a kasashen Masar da kuma Jordan, suna so ko basa so.
Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto kungiyar tana fadar haka a yau Laraba. Ta kuma kara da cewa. Mutanen gaza basa son rabuwa da kasarsu, ta kaka da kakanni. Kuma suna maraba da dukkan shawarorin da kasashe larabawa da sauran kasashe duniya zasu bayar, don ganin an sake gina Gaza ba tare da an kori falasdinawa daga kasarsu ba.
A wani Labari kuma shugaban kasar Amurka ya bawa falasdinawa a Gaza nan da ranar Asabar mai zuwa, na su saki dukkan yahudawan da suka rage a hannunsu ko kuma aka kawo karshen tsagaita wuta tsakaninsu da HKI.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hamas: Za A Mika Gawawwakin ‘Yan Mamaya Da Kuma Fursunoni Rayayyu A Ranakun Alhamis Da Asabar
Shugaban kungiyar Hamas Khalilul-Hayyah, ya fadi cewa; A ranakun Alhamis da Asabar masu zuwa ne za a mikawa ‘yan mamaya fursunoni rayayyu da kuma wasu gawawwaki a cikin bude wani shafin na musaya.
A jiya Talata ne dai Khalilul-Hayyah ya sanar da cewa, a bisa yadda aka cimma matsaya a musayar farko da aka yi, a cikin mako na shida daga kulla yarjejeniya, za a shiga wani sabon shafin na gaba na musayar fursunoni.
Khalil Hayya ya kuma ce a ranar Asabar din mai zuwa ne za a mika sauran fursunoni rayayyu da su ka saura, kamar yadda aka cimma matsaya da adadinsu shi ne 6, biyu daga cikinsu ana rike da su ne tun 2014, yayin da ‘yan mamaya za su saki sauran fursunonin da suke rike da su.
Shugaban na kungiyar Hamas ya bayyana hakan da cewa, yana nuni da yadda kungiyar take aiki da yarjejeniya, tare da yin kira da a tilasta HKI ta yi aiki da sharuddan yarjejeniyar ba tare da jan kafa ba. Haka nan kuma ya bayyana cewa kungiyar ta Hamas tana cikin shirin ko-ta –kwana na shiga shafi na gaba wanda shi ne dakatar da yaki da kuma janyewar sojojin mamayar daga Gaza.