Shugaban Kasar Amurka Ya Sake Jaddada Matsayinsa Dangane Da Gaza A Ganawarsa Da Sarkin Jordan
Published: 12th, February 2025 GMT
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya kara jaddadawa Sarkin Jordan Abdullahi II kan shirinsa na kwace yankin Gaza daga hannun Falasdinawa, sannan ya maida shi wurin shakatawa, da kuma kan cewa kasar Jordan da Masar ne zasu dauki nauyin kula da Falasdinawa kimani miliyon 2 a Gaza a cikin kasashen su.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Trump yana fadar haka a ganawarsa da Sarkin a birnin Washington a yau Laraba.
A nashi bangaren Sarkin kasar ta Jordan ya bayyana cewa yana ganin kasashen larabawa zasu dauki mataki guda ne a cikin wannan al-amarin, sannan zasu ji ta bakin Yerima Muhammad bin Salman na kasar Saudiya da kuma Shugaba Abdul Fattah Assisi na kasar Masar, wadanda suke da shawarorin da zasu gabatar dangane da wannan matsalar.
Sarkin ya kara da cewa a halin yanzu dai kasarsa za ta dauki yara kanana kimani 2000 marasa lafiya, wadanda suke fama da cutar kansa a Gaza don jinyarsu a kasar Jordan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran: Himmati Yana Halattar Taro Dangane Da Matsalolin Da Suka Addabar Kasashe Masu Tasuwa
Ministan tattalin arziki na kasar Iran Abdunnaser Himmati yana halatan taro dangane da matsaloli da kuma dammakin da kasashen masu tasowa suka fama da su a birnin Riyad na kasar Saudiya.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa Himmati yana halattan wannan taro na kwanaki biyu ne tare da gayyatar tokwaransa na kasar Saudiya da kuma shugaban asusun lamuni ta duniya wato IMF.
Labarin ya kara da cewa gwamnatin JMI dai tana kokarin ganin ta kyautata dangantaka ko ta ina da kasashen larabawa na yankin tekun da sauran makobta.
Taron ya hada da ministan kudi na kasar Saudiya, gwamnann babban bankin kasar, da kuma wadanda suke ruwa da tsaki a harkkin kasuwanci na kasar ta saudia, sun hadu da tokwarorinsa na Iran inda suka tattauna kan al-amuran tattalin arziki a tsakaninsu.
Himmati ya bukaci karin hadin kai da kasar saudiya don zuba jari a fannoni daban-daban a kasar Iran. Har’ila yau sun tattauna batun harkokin kudade a lokacin ayyukan hajji.