Jagoran Ya Ce: Fitowar Mutane A Ranar 11 Ga Watan Fabrayru Alamace Ta Hadin Kan Kasa Sannan Jawabi Ga Barazanar Da Kasar Take Fuskanta
Published: 12th, February 2025 GMT
A lokacinda yake ganawa da masana masu fasaha a masana’antun makamai na kasar da kuma manya-manyan Jami’an sojojin Kasar Iran, Jagoran Juyin Juya Halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa fitowar mutane a zanga-zangar cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar, a ranar litinin da ta gabata, wata alama ce ta hadin kan mutanen kasar Iran, har’ila yau jawabi ne ga barazanar da makiya JMI suke mata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jagoran yana fadar haka bayan ya zagaya ya ga sabbin makamai wadanda masana’antun makamai na kasar suka kera. Ya kuma yaba da irin ci gaban da masana’antun suka samu.
Imam Khaminae ya kuma yaba da ayyukan da masu fasaha da suka kerasu wadannan makamai.
Sabbin makaman da aka baje kolinsu dai, sun hada da garkuwan makamai masu linzami wadanda zasu iya kare sararin samaniyar kasar.
Da kuma ci gaban da aka samu a bangaren garkuwan sararin samaniyar kasar. Har’ila yau da kuma ci gaban da aka samu a bangaren sojojin ruwa.
Daga karshe jagoran ya jinjinawa ma’aikatar tsaron kasar kan irin ci gaban da aka samu, musamman a dai dai lokacinda kasar take fuskantar Barazana. Daga karshe yace: Lalle su zage dantse don gani barazan da kasar take fuskanta a yanzu, da kuma nan gaba sun magancesu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tunisiya : Kaïs Saïed, ya kori firaministansa Kamel Madouri
Shugaba Kaïs Saïed na Tunisiya ya kori firaministan kasar Kamel Madouri, da aka nada a watan Agustan da ya gabata yayin wani gagarumin garanbawul a majalisar ministocin kasar a daren jiya Alhamis.
Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce an maye gurbin firaministan kasar Madouri nan take inda aka maye gurbinsa da Sarra Zaafrani Zenzri, ministar kayan aiki.
Sanarwar ta ce sauren mambobin gwamnatin zasu ci gaba da aikinsu.
Garan bawul na shugaban kasar ta Tunisia a baya baya nan shi ne na ranar 6 ga watan Fabrairu inda ya sallami ministan kudinsa Sihem Boughdiri Nemsia da tsakar dare, tare da maye gurbinsa da alkalin kotun Michket Slama Khaldi.