Darajar Jigilar Kayayyakin Jama’a A Sin Ta Kai Yuan Triliyan 360.6 A 2024
Published: 12th, February 2025 GMT
Alkaluma daga hukumar kula da jigila da sayen kayayyaki ta kasar Sin sun nuna cewa, darajar jigilar kayayyakin jama’a da aka yi a kasar Sin a shekarar 2024, ya karu da kaso 5.8 zuwa yuan triliyan 360.6, kwatankwacin dala triliyan 50.28, idan aka kwatanta da 2023.
Zuwa karshen 2024, kasar ta samar da cibiyoyi 151 na jigilar kayayyaki na kasa da sama da wuraren ajiyar kayayyaki 2,500 a kasashen waje.
A cewar Hu Han, jami’i a cibiyar tattara bayanan da suka shafi jigila ta kasar, ingantawa kayayyakin aiki da suka shafi jigila da daukaka tsarin hanyoyin jigila sun bunkasa ware albarkatu ga bangaren da kuma hade yankunan kasa da kasa. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa; Yahudawan Sahayoniyya Sun Kasa Murkushe Gwagwarmaya
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta fuskanci cewa dole ta mika wuya tare da amincewa da sulhu da ‘yan gwagwarmaya da ta nemi murkushe su
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya ba su cimma ko daya daga cikin munanan manufofinta ba, kuma daga karshe ya zama tilasta su mika wuya tare da amincewa da sulhu da bangarorin da suke son kawar da su.
Babban sakataren kungiyar jihadul-Islami ta Falasdinu Ziyad Nakhalah, da ya ziyarci birnin Tehran a karkashin jagorancin wata tawaga don tuntubar hukumomin kasar Iran ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sayyid Abbas Araqchi a yammacin jiya Talata.
Haka nan yayin da yake ishara da halaltacciyar gwagwarmayar da al’ummar Falastinu suke yi na neman ‘yancin kai daga ‘yan mamayar yahudawan sahayoniyya tsawon shekaru 80 da suka gabata, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya taya al’ummar Falasdinu murnar samun nasara mai dimbin tarihi da suka samu da kuma juriya kan kisan kiyashin da suka fuskanta daga yahudawan sahyoniya a Gaza na tsawon watanni goma sha shida.