Taro kan fasahar kirkirarriyar basira ta AI da ya gudana a Paris na Faransa, ya ja hankalin duniya. Masu rattaba hannu 61 ciki har da Faransa da Sin da India, sun fitar da wata sanarwa cewa za su nace wajen raya wannan fasaha bisa ka’ida ba tare da rufa rufa ba, kuma ta kowane bangare.

Kimiyya ba ta da iyaka.

Idan muka waiwayi ci gaban bil adama, ba a taba raba kowace nasara da aka samu a binciken kimiyya da kirkire kirkiren fasaha da hadin gwiwa da musaya tsakanin kasa da kasa ba. Gwamnatin Sin na goyon bayan ci gaban kimiyya da fasaha ta kowane bangare, kuma a shirye take ta gabatar da gogewarta a fannin ga duniya. DeepSeek, samfurin AI na kasar Sin, ya rungumi tsarin bayyana asalin samar da fasahar. Wannan mataki, ya dace da yanayin da ake ciki yanzu.

An ga fitowar fasahar kirkirarriyar basira, kuma yadda za a yi kyakkyawan amfani da wannan karfi, batu ne dake gaban dukkan kasashen duniya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Tara Daga N100,000 Kan Amfani Da Mitar Wutar Lantarki Ta Ɓarauniyar Hanya – NERC

Tara Daga N100,000 Kan Amfani Da Mitar Wutar Lantarki Ta Ɓarauniyar Hanya – NERC

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hamas Ta Ce Tana Iya Sakin Dukkan Fursinonin Yahudawa Gaba Daya A Lokaci Guda
  • Gwamnati Za Ta Haramta Amfani Da Tankoki Masu Ɗaukar Lita 60,000 Aiki Daga Maris 1
  • Matasan Jihar Jigawa Sun Karrama Gwamna Umar Namadi
  • UNICEF Ya Bukaci Hadin Kai Don Inganta Rayuwar Kananan Yara A Jigawa
  • Tara Daga N100,000 Kan Amfani Da Mitar Wutar Lantarki Ta Ɓarauniyar Hanya – NERC
  • Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alhinin Rasuwar Edwin Clark
  • Daga Munich Zuwa Addis Ababa, Ci Gaban Kasashe Daban Daban Na Tabbata
  • Sojojin HKI Sun Fara Ficewa Daga Wasu Wurare A Kudancin Kasar Lebanon
  • FG Ta Jaddada Bukatar Samarda Sabbin Ka’idojin Visa Domin Taimakawa Kasuwancin A Duniya
  • Hukumar Kula Da Ayyukan Duba-gari Ta Kasa Za Ta Karrama Shugaba Tinubu