Leadership News Hausa:
2025-03-23@04:19:08 GMT

CGTN Ya Shirya Bikin Musayar Al’adu A Birnin Harbin Na Sin

Published: 12th, February 2025 GMT

CGTN Ya Shirya Bikin Musayar Al’adu A Birnin Harbin Na Sin

A yau Laraba, kafar yada labarai ta CGTN ta hada gwiwa da tashar watsa labarai ta lardin Heilongjiang na kasar Sin ta kamfanin CMG, wajen shirya wani bikin musayar al’adu na kasa da kasa, wanda ya shafi gasar wasannin kankara ta nahiyar Asiya dake gudana a Harbin, gami da bikin fitilu na gargajiyar kasar Sin.

Mahalartar bikin sun hada da ‘yan wasa da ‘yan jaridu na kasashen nahiyar Asiya daban daban. (Bello Wang)

 

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Najeriya: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Watsi Da Zargin Kisan Kiristoci A Kasar

Fadar Shugaban Kasar Nijeriya, ta yi watsi da rahoton baya-bayan nan da kwamitin hulda da kasashen wajen Amurka ya fitar, wanda ya kafa hujja da amincewar majalisar dokokin kasar, na zargin kakaba wa wasu kiristoci takunkumi a kasar.

Mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin siyasa, Daniel Bwala, ya bayyana rahoton a matsayin wanda ba shi da tushe da makama, yana mai jaddada cewa; tun bayan lokacin da Shugaba Tinubu ya dare kan kujerar mulki a ranar 29 ga Mayun 2023, al’amuran cin zarafi, musamman ta fuskar addini suka yi matukar ja da baya.

Bwala, ya yi wannan furuci ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, wato na D; yana mai jaddada cewa, gwamnatinsu mai ci yanzu; ta himmatu wajen kokarin daidaita addinai a matsayin abu guda.

“Gwamnatin Bola Tinubu, koda-yaushe na kokarin bai wa addinai muhimmanci na musamman. Tun daga ranar 29 ga Mayun 2023, daidai lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya hau kan karagar mulki, ba a taba samun wasu matsaloli na tsananta wa Kiristoci a ko’ina a fadin wannan kasa ba”, kamar yadda ya rubuta.

Ya jaddada cewa, Nijeriya ta kasance kasa mai dauke da addinai daban-daban, sannan a kowane lokaci gwamnati na kokarin samar da zaman lafiya a tsakanin wadannan addinai.

Martanin da Fadar Shugaban Kasar ta mayar, ya biyo bayan nuna damuwa a kan matakin da Majalisar Dokokin Amurka ta dauka na amincewa da takunkumin da aka kakaba wa Nijeriya, bisa zargin kashe Kiristoci.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wang Yi: Kasar Sin Na Da Kwarin Gwiwa Kan Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Japan Da Koriya Ta Kudu  
  •  Haaretz: Sojojin Isra’ila Suna Kan Shirya Kai Wa Gaza Hari Ta Kasa
  • Kwana Daya Bayan Kwace Fadar Shugaban Kasa, Sojojin Sudan Sun Kwace Babban Bankin Kasar
  • Masarautar Bauchi Ta Sauya Shawara: Za A Yi Hawan Daushe
  • Najeriya: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Watsi Da Zargin Kisan Kiristoci A Kasar
  • Sojojin Sudan Sun Kwace Iko Da Fadar Shugaban Kasa A Birnin Khartum
  • Shugaban Kasar Iran Ya Bukaci Hadin Kai Tsakanin Iraniyawa Saboda Amfanin Kasar
  • ’Yan adawa sun shirya ƙalubalantar Tinubu a zaɓen 2027 – Atiku
  • Sin: Shingayen Kasuwanci Suna Illata Wadatar Tattalin Arzikin Duniya
  • Masarautun Kano Zasu Gudanar da Hawan Daba A Bikin Sallah Karama