NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Durƙusar Da Gidajen Rediyo A Arewa
Published: 13th, February 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Rediyo na daga cikin kafofin da al’umma da dama suka dogara da su don jin labarai, shirye-shirye da kuma samun nishadi.
Rediyo na taka muhimmiyar rawa wajen wayar wa da al’umma da dama kai musamman duba da yadda aka bayar da shaidar cewa tafi kowace kafa saurin yaɗa bayanai ba a cikin birane ba, har ma da yankunan karkara.
Sai dai a wannan gaɓa ana ganin gidajen rediyo a Arewacin ƙasar nan na samun koma baya, la’akari da yadda a wasu lokutan wasu suke rufe harkokinsu su ɓace ba tare da jin ɗuriyarsu ba.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Ci-gaban Da Hukumomin Raya Shiyyoyi Za Su Samar
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A kwanakin baya ne dai Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙirƙiro sababbin hukumomin raya shiyyoyin ƙasar nan da nufin kawo musu ci-gaba.
Gabanin ƙirƙirar waɗannan hukumomin, gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ce ta fara kirkirar hukumar raya yankin Neja Delta bayan wasu ƙalubale da suka dabaibaye yankin.
Na baya-bayan nan ita ce Hukumar Raya yankin Arewa ta Tsakiyar ƙasar nan bayan da ’yan yankin suka nace da yin ƙorafin cewa an mayar da su saniyar ware.
NAJERIYA A YAU: Dalilan Saukar Farashin Kayan Masarufi A Kaswanni DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar HausaShirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan irin ci-gaban da waɗannan hukumomin raya shiyyoyi za su samar ga al’ummar ƙasa.
Domin sauke shirin, latsa nan