AU Na Tattaunawa Kan Batun Ci Gaban Nahiyar Da Zaman Lafiya
Published: 13th, February 2025 GMT
An bude babban taron majalisar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka, watau AU karo na 46, a hedkwatar kungiyar da ke Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, inda taron ya jaddada bukatar gaggauta karfafa kokarin da ake yi na bunkasa ci gaban nahiyar, da kwanciyar hankali.
Taron na kwanaki biyu, wanda ya kunshi ministocin harkokin waje na mambobin kungiyar ta AU, ana gudanar da shi ne a karkashin taken da kungiyar ta AU ta fitar na shekarar 2025 : “Adalci ga ‘yan Afirka ta hanyar biyan diyya.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban hukumar kula da harkokin AU, Moussa Faki Mahamat, ya jaddada muhimmancin samar da kokarin hadin gwiwa domin inganta zaman lafiya da tsaro a fadin nahiyar.
Ya kuma bayyana wajibcin gudanar da shugabanci nagari, da bunkasa tattalin arziki da zamantakewar jama’a, da samar da isassun kudade masu dorewa, da sake fasalin hukumomin AU.
Kazalika, ya jaddada bukatar daukaka matsayi da hadin kan Afirka a fagen harkokin duniya.
Bugu da kari, taron zai yi nazari kan daftarin ajanda da shawarwarin taron da za a yi na shugabannin kasashe da gwamnatocin kungiyar ta AU karo na 38, wanda aka shirya gudanarwa a tsakanin ranakun 15 da 16 ga watan Fabrairun nan.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kungiyar ta
এছাড়াও পড়ুন:
Brice Ologui Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Gaban Da Kashi 90.35% A Jiya Lahadi
Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Gabon wanda kuma ya jagoranci juyin mulkin da aka yiwa Ali Bongo tsahon shugaban kasar ya lashe zaben da aka gudanar a jiya Lahadi tsakanin yan takara 7 har da shi.
Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News” ya bayyana cewa Oligui dan shekara 50 a duniya, shi ne babban dogarin sojoji masu tsare fadar shugaban kasar Gaban, a lokacinda ya jagoranci juyin mulkin da ya kawo karshen mulkin da yan gidan Bogo suka yi na shekaru kimani 50 a kasar.
Labarin ya kara da cewa kashi 2/3 na mutanen Gabon wadanda yawansu bai fi miliyon 2.3 ba suna cikin talauci a cikin kasa wacce take da arziki mai yawa.
Brice zai jagoranci kasar na tsawon shekaru 7 masu zuwa kuma yana iya sake shi takarar shugabancin kasa karo na biyu.
Yan takara 6 ne suka tsaya tare da Brice amma mai binsa bai sami fiye da kashi 3 % na kuri’un da aka kada ba sannan yawan fitowar mutane masu zabe ya kai kashi 70.4% wanda ya nuna cewa an sami sauyi babban a cikin harkokin siyasar kasar ta Gabaon.