HausaTv:
2025-02-20@08:55:22 GMT

Iran Da Turkmenistan Na fatan Karfafa Alakarsu

Published: 13th, February 2025 GMT

Kasashen Iran da kuma Turkmenistan sun kudiri anniyar karfafa alakar dake a tsakaninsu a bangarori daban-daban, in ji shugaba Masoud Pezeshkian.

A wata ganawa da ya yi da ministan harkokin wajen Turkmenistan Avazgeldyevich Meredov a birnin Tehran, shugaban na Iran ya ce “An bayar da umarnin da suka wajaba ga hukumomin da abin ya shafa domin nazarin bangarorin da za su kara yin hadin gwiwa da gwamnatin Turkmenistan.

Pezeshkian ya kuma yi ishara da wani taro da za a yi a birnin Teheran na tekun Kasbiya, inda ya kara da cewa Iran na kokarin fadada alaka a tsakanin kasashen Caspian bisa zaman lafiya, abokantaka, da kyakkyawar makwabtaka.

A yayin wannan ganawar, ministan harkokin waken Turkmenistan ya yaba da yarjejeniyoyin da aka kulla tsakanin kamfanonin Iran da Turkmen a fannonin sufuri da makamashi, ya kuma yi kira da a kara yin hadin gwiwa tsakanin Iran da Turkmenistan a dukkan bangarori.

Meredov ya kuma bayyana fatan cewa, gudanar da kwamitin hadin gwiwa kan harkokin tattalin arziki zai inganta dangantakar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

Dangantaka tsakanin kasashen biyu na da matukar muhimmanci ga gwamnatin kasar Turkmenistan, kuma muna son fadada huldar dake tsakanin kasashen biyu ta kowane fanni.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Wang Yi Ya Bayyana Ra’ayin Sin Kan Yadda Za A Karfafa Huldar Cude-Ni-In-Cude-Ka A Duniya

A karshe dai, ya nanata muhimancin raya karfin kasa da kasa ta hanyar aiwatar da ayyuka masu alaka da hakan.

Wang Yi ya jaddada cewa, kasar Sin tana fatan yin hadin gwiwa da sassa daban daban, domin bude sabon babin raya huldar cude-ni-in-cude-ka, tare da kafa tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa mai inganci.

Bayan taron, ya kuma amsa tambayoyin ‘yan jaridu, game da yadda kwamitin sulhu na MDD zai karfafa kwarewarsa ta gudanar da ayyuka, da matsayin kasar Sin kan batun Gaza da dai sauransu. (Mai Fassara: Maryam Yang)

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Turkiya Ta Karbi Bakuncin Tattaunawar Sulhu Tsakanin Habasha Da Somaliya
  •  Jagora: Siyasar Kasar  Iran  Ta Ginu Ne Akan Kyautata Alaka Da Kasashen Makwabta
  • Wang Yi Ya Bayyana Ra’ayin Sin Kan Yadda Za A Karfafa Huldar Cude-Ni-In-Cude-Ka A Duniya
  • Shugaban Kasar Iran Ya Tattauna Da Sarkin Kasar Qatar Kan Muhimmancin Hadin Gwiwa Da Taimakekkeniya Tsakaninsu
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa; Yahudawan Sahayoniyya Sun Kasa Murkushe Gwagwarmaya
  • Kasashen Rasha Da Amurka Sun Kuduri Anniyar Kawo Karshen Yaki A Ukraine
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana Irin Gagarumar Rawar Da Iran Ta Taka A Fegen Tsaro Yakin Tekun Pasha
  • Ministan Harkokin Waje Iran Ya Jaddada Cewa Iran Ba Zata Tattauna Da Amurka A Karkashin Takunkumai ba
  • Sarkin Qatar Zai Zayarci Tehran A Gobe Laraba
  • IRGC: Za Mu Kai Farmakin “ Wa’adus-Sadik” Na 3 Akan ‘Yan Mamaya