HausaTv:
2025-03-23@04:19:08 GMT

Hamas Ta Yi Watsi Da Barazanar Amurka Da Isra’ila Kan Musayar Fursunoni

Published: 13th, February 2025 GMT

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi watsi da barazanar da Isra’ila da Amurka ke yi kan batun musayar fursunoni.

Kakakin kungiyar Hamas Hazem Qassem ya fada cewa Isra’ila tana kaucewa aiwatar da wasu tanade-tanade na yarjejeniyar tsagaita bude wuta,” yana mai gargadin cewa ba za a sako mutanen da ake garkuwa da su ba idan ba Isra’ila ta mutunta yarjejeniyar ba.

Qassem ya ce, “Matsayinmu a fili yake, kuma ba za mu amince da barazanar Amurka da Isra’ila ba,” in ji Qassem, bayan firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu ya yi barazanar komwa yaki idan har ba a sako mutanen da aka kama ba zuwa ranar Asabar.

A ranar Laraba, ministan harkokin soji na gwamnatin ya yi gargadin cewa Isra’ila za ta sake fara yakin Gaza idan Hamas ta gaza sakin ‘yan Isra’ila da take tsare da su kuma a wannan karon za ta yi barna.

“Sabon yakin na Gaza zai sha bamban kuma mai tsanani da wanda ya gabata kafin tsagaita bude wuta, kuma ba zai kare ba sai mun fatattaki Hamas da kuma sako dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su,” in ji Isra’ila Katz a cikin wata sanarwa.

“Hakan kuma zai ba da damar tabbatar shirin shugaban Amurka Donald Trump game da Gaza,” in ji Katz, yayin da yake magana kan shirin shugaban Amurka na mamaye yankin Falasdinu.

A baya dai kungiyar Hamas ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, wata tawaga karkashin jagorancin babban mai shiga tsakani ta isa birnin Alkahira inda ta fara ganawa da jami’an Masar” suna sa ido kan yadda ake aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

A cikin kwanaki 3 Falasdinawa 605 sun yi shahada a kisan kiyashin Isra’ila a Gaza

Daruruwan Falastinawa fararen hula ne suka yi shahada tun bayan da Isra’ila ta dawo da hare-haren kisan kare dangi a kan al’ummar yankin zirin gaza, matakin day a yi hannun riga baki daya da yarejejeniyar dakatar da bude wuta da aka rattaba hannu a kanta karkashin jagorancin Amurka, Masar da kuma Qatar.

Dakarun mamaya na Isra’ila sun kaddamar da wani farmaki mai matukar muni da manyan makamai a ranar Juma’a a kan yankunan arewa maso yammacin Gaza da suka hada da Sudaniya, al-Karamah, da kuma Beit Lahia, wanda hakan ya yi sanadin shahadar fararen hula masu yawa da suka hada da mata da kananan yara, yayin da kuma wasu daruruwa suka jikkata.

Sojojin Isra’ila sun yi gargadi ga dukkanin Falasdinawa mazauna yankunan  Sultan, Karama, da Awda da ke arewacin zirin Gaza, inda suka bukace su da su bar gidajensu, su koma zuwa yankunan kudancin Gaza.

Majiyoyin cikin gida sun ba da rahoton cewa, an kai wasu wadanda suka samu raunuka da dama da suka hada da wanda ke cikin mawuyacin hali zuwa asibitin Indonesiya da ke arewacin Gaza.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Haaretz: Sojojin Isra’ila Suna Kan Shirya Kai Wa Gaza Hari Ta Kasa
  • MDD da EU sun yi tir da wargaza yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da Isra’ila ta yi
  • Iran da UAE sun kirayi Isra’ila da Amurka da su kawo karshen hare-harensu a Gaza da Yemen
  • Saree: Filin jirgin saman Ben Gurion ba shi da aminci har sai an kawo karshen yakin Isra’ila a Gaza
  • A cikin kwanaki 3 Falasdinawa 605 sun yi shahada a kisan kiyashin Isra’ila a Gaza
  • Jagora: Amurka Ta Kwana Da Sanin Cewa Ba  Wata Riba Da Za Ta Ci Ta Hanyar Yi Wa  Iran Barazana
  • An kori shugaban hukumar leken asiri ta cikin gidan Isra’ila
  • Zargin Kisan Kiristoci A Nijeriya: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Watsi Da Rahoton Amurka
  • Hare-Haren Isra’ila Cikin Dare Sun Hallaka Mutum Aƙalla 50 A Gaza
  • Kungiyar Hamas Ta Ce Falasdinawa Ba Za Su Bar Kasarsu Ba, Ko Da Son Ransu Ko Da Karfi