Aminiya:
2025-03-23@04:23:46 GMT

Yanzu Yanzu: Shugaban Hukumar Kwashe Shara ta Kano REMASAB Haruna Zago ya rasu

Published: 13th, February 2025 GMT

Shugaban Hukumar Kwashe Shara ta Jihar Kano Ambasada Haruna Zago ya rasu bayan fama da rashin lafiya.

Ɗaya daga cikin ma’aikatan hukumar ne ta tabbatar da haka  Hausa rasuwar Haruna Zago a asibiti.

A ranar 5 ga watan Yulin shekarar 2023 Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya naɗa Haruna Zago a matsayin Shugaban Hukumar REMASAB

.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ɗan Zago Ɗanzago Haruna Zago

এছাড়াও পড়ুন:

Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna Ta Bukaci Taimakon NAMA Don Gudanar Da Aikin Hajjin Bana Cikin Nasara 

 

 

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta roƙi Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Najeriya (NAMA) ta ci gaba da ba da goyon baya domin tabbatar da nasarar gudanar da aikin Hajjin bana.

 

A ziyarar ayarin hukumar ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gudanarwa, Malam Baba Mohammed Rufa’i, wanda ya wakilci Shugaban Hukumar, Malam Salihu Abubakar, ta kai ziyara ga jami’an NAMA a Filin Jirgin Sama na Hassan Usman Katsina da ke Kaduna.

 

A yayin ziyarar, Malam Salihu Abubakar ya yaba wa NAMA bisa gudunmuwar da take badawa wajen nasarar hajjojin da suka gabata, inda ya roƙi irin wannan haɗin gwiwa a bana.

 

Ya jaddada muhimmancin samun ingantattun hanyoyin sufuri tare da roƙon NAMA ta tabbatar da samar da duk wani kayan aiki da ake bukata domin kauce wa cikas yayin jigilar alhazai.

 

A nasa jawabin, Manajan Harkokin Zirga-zirgar Jiragen Sama na filin jirgin, Alhaji AbdulMajid Mohammed, ya tabbatar da aniyar NAMA na ci gaba da tallafa wa aikin jigilar alhazan Jihar Kaduna.

 

Ya bayyana cewar har yanzu akwai matsalar ginin sabon hasumiyar kula da zirga-zirga da ba a kammala ba, yana mai ƙarin bayani cewa yawan katsewar wutar lantarki na kawo cikas, wanda ya sa yanzu filin jirgin ke aiki ne kawai kafin ƙarfe 5 na yamma.

 

Duk da waɗannan ƙalubalen, Alhaji AbdulMajid ya tabbatar wa Hukumar Jin Daɗin Alhazai cewa NAMA na da ƙudurinsa na ganin cewa aikin jigilar alhazan Kaduna zai kasance cikin tsari da kwanciyar hankali.

 

Ya tabbatar da cewa ana ɗaukar dukkan matakan da suka dace domin rage yiwuwar samun cikas da kuma tabbatar da nasarar tafiyar Hajjin bana.

 

Rel/Adamu Yusuf

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Nasiru Ahali Shahararren masanin masana’antu a Kano ya rasu
  • Hajjin Bana: Maniyata 3, 155 Suka Yi Rijista a Kano
  • An kori shugaban hukumar leken asiri ta cikin gidan Isra’ila
  • Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna Ta Bukaci Taimakon NAMA Don Gudanar Da Aikin Hajjin Bana Cikin Nasara 
  • Gobara ta ƙone gidaje tare da asarar dukiya a Gombe
  • Sanƙarau ta kashe mutum 55 saboda rashin tsafta a Kebbi
  • Sabon Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano Yayi Alkawarin Inganta Tsaro
  • Sojoji Sun Ceto Mutanen Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina Da Zamfara
  • Gobara Ta Babbake Wani Shago A Jihar Kwara
  • Fashewar Tanka: Asibitoci sun cika da mutane a Abuja