Miƙa makaman ’yan bindigar Katsina ya bar baya da ƙura
Published: 13th, February 2025 GMT
A karo na biyu a kasa da wata daya wasu ’yan bindiga sun mika makamansu ga sojoji, a wani kokari na samar da zaman lafiya.
Aminiya ta ruwaito yadda a a ranar 19 ga watan Janairun 2025, ’yan bindiga suka sallama makamansu da mutanen da suka yi garkuwa da su, a wani zaman sulhu da aka yi da su a yankin Ƙaramar Hukumar Batsari ta Jihar Katsina.
A gefe guda kuma wasu kuma na zargin Gwamnatin Tarayya Nana hannu wajen yin sulhu da ’yan ta’addan ta bayan fage domin a sami zaman lafiya a Jihar.
Al’ummar Batsari sun halarci taron mika malaman inda sun bayyana ra’ayoyi mabanbanta. Wasu na ganin abin yabo da da ta kamata a ba wa goyon, wasu kuma na ganin sa a matsayin tarin shayi, saboda an mayar da al’ummar da hare-haren suka shafa saniyar ware.Wani mazaunin yankin ya ce, “Ba a gayyace mu ba amma na je na ga abin da aka yi. Kimanin motoci takwas na APC da hiluxs ɗauke da sojoji da ’yan sanda da jami’an tsaron CWC da ’yan banga.
“Na ga ’yan bindigar sun miƙa wa sojoji bindigogi biyu ƙirar Machine Gun sun neman a basu damar shiga garuruwanmu da kasuwanninu ba tare da wani ƙaido ba.
“Duk da cewa ba duk makamansu suka miƙa ba, amma na yi imani abu mai kyau ne kuma ya kamata a dama da duk hukumomin tsaro,” in ji shi. Wani ɗan yankin kuma ya ce babu yadda za a yi sulhun ya yi nasara ba tare an sanya mutanen ya yankunan da abin ya shafa ba. Ya ce, “a na farkon da ka yi, kawai jerin gwanon motocin jami’an tsaro muka gani suna zuwa wurin. Shi ne wasunsu suka je, inda suka ga ’yan bindiga sun mika musu bindigogi biyu. Haka kuma aka yi a na biyun da ka yi jiya. “Amma ban je na jiyan ba, saboda ina tunanin babu abin da zai tsinana,” in ji shi. Gwamna Radda ya jaddada matsayinsa Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, wanda ya ziyarci Batsari ya jaddada matsayinsa cewa gane da sulhu da ’yan bindigar cewa gwamnatinsa ba za ta roƙe su ko ta lallashe su su miƙa makamansu ba.Ya ce “mun sha faɗa cewa babu ɗan bindigar da za mu je mu roƙe shi don a samu zaman lafiya. Amma idan su da kansu suka zo suka miƙa wuya za mu karɓe su,” in ji a yayin wani gangamin yaƙin nemba Batsari gabanin zaɓen ƙananan hukumomin jihar da za a gudanar ranar Asabar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Batsari yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
MDD Ta Bukaci Taimako Dangane Rikicin Sudan Wanda Ya Isa Kasar Chadi
Shugaban hukumar yan gudun hijira na MDD Filippo Grandi wanda ya ziyarce sansanonin yan gudun hijira na kasar Sudan a Chadi ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen duniya su taimaka don kula da bukatun yan kasar sudan wadanda suke gudun hijira a kasar Chadi.
Grandi ya kara da cewa akwai bukatar agaji da gaggawa zuwa kasar Chadin da kuma sauran kasashen da suke daukar nauyin yan gudun hijira na sudan. A halin yanzu dai ana ganin mutane kimani 20,000 ne suka rasa rayukansu, sannan wasu da dama suka ji rauni sannan wasu kuma suka zama yan gudun hijira.