Malaman Makaranta Da Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi Sun Tsunduma Yajin Aiki A Abuja
Published: 13th, February 2025 GMT
Ƙungiyar malamai ta NUT-FCT da ma’aikatan ƙananan hukumomi na NULGE sun fara yajin aiki na dindin a yau Alhamis, sakamakon gazawar shugabannin ƙananan hukumomi wajen aiwatar da sabon albashi mafi ƙarancin na ₦70,000 da aka amince da shi tun Disamba 2024.
Ƙungiyoyin sun koka cewa duk da cewa sauran ma’aikatan FCT sun fara karɓar sabon albashin, an bar malaman firamare da ma’aikatan ƙananan hukumomi a baya.
A sakamakon yajin aikin, an rufe makarantu a sassa daban-daban na FCT, inda malamai suka sallami ɗalibai. Wata malama, Mrs. Ene Igado, ta ce malaman firamare na L.E.A ana yi musu babbar wariya idan aka kwatanta da takwarorinsu na UBEB, duk da cewa su ne ke yin mafi yawan aiki.
এছাড়াও পড়ুন:
Saudiyya ta bai wa Kano da Abuja tallafin dabino
Gwamnatin Saudiyya ta bai wa babban birnin Nijeriya Abuja da kuma Jihar Kano tallafin tan 100 na dabino.
Ofishin Jakadancin Saudiyya ya gudanar da gagarumin bikin bayar da tallafin dabinon ne a wani ɓangare na ayyukan agaji da yake yi duk shekara.
Shirin wanda Cibiyar Bayar da Agaji da Jin Ƙai ta Sarki Salman (KSrelief) ta ɗauki nauyin gudanarwa, na da nufin tallafa wa iyalai masu ƙaramin ƙarfi a faɗin ƙasar da kuma ƙarfafa danƙon zumunci tsakanin ƙasashen biyu.