Sojoji Sun Yi Nasara Akan ‘Yan Ta’adda A Zamfara Da Sakkwato.
Published: 13th, February 2025 GMT
Dakarun Operation Fansan Yamma sun dakile ayyukan ta’addanci a jihohin Zamfara da Sokoto daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Fabrairun 2025.
A cewar wata sanarwa da kodinetan cibiyar yada labarai na Operation Fansan Yamma Laftanar Kanar, Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce harin ya yi sanadin fatattakar ‘yan ta’adda da dama da suka hada da wasu manyan ‘yan ta’adda.
Ta ce aikin na inganta tsaron rayuka da dukiyoyi a yankin.
Sanarwar ta bayyana cewa, a tsawon wannan lokaci, sojoji sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda da dama da suka hada da sarakuna irin su Kachalla Na Faransa, Dogon Bakkwalo, Auta Gobaje da Dan Mai Dutsi da dai sauransu.
Ya bayyana cewa, an kawar da da yawa daga cikin wadannan mutane a wani kazamin fada da aka yi a kananan hukumomin Shinkafi da Zurmi na jihar Zamfara da kuma karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto.
Baya ga kawar da wasu manyan mutane, sojojin sun kai farmaki kan maboyar ‘yan ta’adda, inda ta ce an lalata maboyar ‘yan ta’adda kimanin 40, a cikin yankunan Tungar Fulani, Unguwar Goga, Tudun Gangara, da Gidan Maji.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, wannan gagarumin farmakin na da matukar muhimmanci wajen dakile ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma.
Sojojin sun kuma samu nasarar kwato tarin makamai da alburusai, wanda zai zama muhimmi wajen hana kai hare-hare.
Sanarwar ta jaddada cewa, Operation Fansan Yamma na ci gaba da jajircewa wajen kawo cikas ga ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso yammacin Najeriya da jihar Neja.
Muna kara jan hankalin jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai kan ‘yan ta’addan da ke gudun hijira har da Bello Turji da mukarrabansa.
Rel/Aminu Dalhatu/WABABE
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Sakkwato Tsaro Zamfara yan ta adda
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa; Yahudawan Sahayoniyya Sun Kasa Murkushe Gwagwarmaya
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta fuskanci cewa dole ta mika wuya tare da amincewa da sulhu da ‘yan gwagwarmaya da ta nemi murkushe su
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya ba su cimma ko daya daga cikin munanan manufofinta ba, kuma daga karshe ya zama tilasta su mika wuya tare da amincewa da sulhu da bangarorin da suke son kawar da su.
Babban sakataren kungiyar jihadul-Islami ta Falasdinu Ziyad Nakhalah, da ya ziyarci birnin Tehran a karkashin jagorancin wata tawaga don tuntubar hukumomin kasar Iran ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sayyid Abbas Araqchi a yammacin jiya Talata.
Haka nan yayin da yake ishara da halaltacciyar gwagwarmayar da al’ummar Falastinu suke yi na neman ‘yancin kai daga ‘yan mamayar yahudawan sahayoniyya tsawon shekaru 80 da suka gabata, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya taya al’ummar Falasdinu murnar samun nasara mai dimbin tarihi da suka samu da kuma juriya kan kisan kiyashin da suka fuskanta daga yahudawan sahyoniya a Gaza na tsawon watanni goma sha shida.